kare batun sayar da hanun jarin kamfanin jirgin kasa | Labarai | DW | 21.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

kare batun sayar da hanun jarin kamfanin jirgin kasa

Ministan kula da sufuri na nan tarayyar jamus Wolfgang Tiefensee,ya kare matsayin gwamnati adangane da shirin sayer da kashi 49 daga cikin 100,na hannun jarin kamfanin jiragen kasa mallakar gwammanti,a mahawarar dake cigaba da gudana a zauren majalisar tarayya.Ya hakikance cewar sayer da da hannayen jarin kamfanin jiragen kasar,zai taimakawa kamfanin inganta ayyukanta,tare da bata damar karawa da sauran takwarorinta na kasashen ketare.A yanzu haka dai kamfanin jiragen kasa na jamus din na fuskantar rigingimu a dangane da bukatun,kungiyar matuka jiragen na karin albashi da kashi 31 daga cikin 100,batu da kamfanin yace bazata yiwu ba.