Karawar Alƙa′ida da sojojin Moritaniya | Labarai | DW | 18.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karawar Alƙa'ida da sojojin Moritaniya

A gumurzun yaƙi da Alƙa'ida a arewacin Afirka, sojojin Moritaniya sun hallaka dakarun ƙungiyar 12

default

Sojojin Moritaniya dake yaƙi da 'yan ta'adda

Sojojin ƙasar Moritaniya sun kara da 'yan ƙungiyar Alƙa'ida a kusa da iyaka da ƙasar Mali, a dai-dai lokacin da ake zargin ƙungiyar da sace wasu ma'aikatan baƙi a ƙasar Nijar. Wani kakakin sojojin Moritaniya ya ce dakarunsu sun hallaka 'yan Alƙa'ida 12 a wani gumurzu da aka yi, kana suma sojojin sun rasa mutane biyu. Tun a jiya dai  jami'an tsaron ƙasar Aljeriya su ka ce ana wata fafatawa tsakanin sojin Moritaniya da 'yan tsagerun Alƙa'ida da ke arewacin Afirka.  Dakarun Moritaniya cikin motoci kimanin 20 su ka shiga faɗan a kilomita 100 daga birnin Timbuktu na ƙasar Mali. Ba'a dai bayyana cewa ko wannan karawa ta na alaƙa da sace turawan Faransa da aka yi a jamhuriyar Nijar ba. Jami'an tsaron Aljeriya suka ce waɗanda suka sace turawan Faransa biyar da wasu mutane biyu 'yan ƙasashen Togo da Madagaska a yankin Arlit dake jamhuriyar Nijar, sun tsallaka da su cikin hamadar ƙasar Mali.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi