Karancin likitoci ya hana yaki da kanjamau | Labarai | DW | 07.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karancin likitoci ya hana yaki da kanjamau

Hukumar lafiya ta duniya, tace karancion likitoci da maaikakan jiyya a koina cikin duniya,suke haddasa rashin samun nasarar yakar cutar kanjamau da sauran manyan cututtaka .

Cikin rahotanta na shekara shekara na 2006,hukumar ta lafiya tace ana bukatar fiye da likitoci miliyan 4 da zasu cike gibin da aka samu,musamman a yankunan karkara na Asiya da Afrika.rahoton yace kashi 3 ne kadai cikin dari na maaikatan jiyya suke nahiyar Afrika,yace daya daga cikin likitoci 4 na afrika sun gudu zuwa kasashe masu tasowa.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya Lee Jong-wook yace muddin dai baa baa gaggauta samarda kudi ba yanzu,da wuya hukumar ta cimma burinta na kawarda talauci musamman ta fannin kiwon lafiya.