1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kara tabarbarewar lamura a kasar Burundi

Salissou BoukariJanuary 15, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwarta kan halin da ake ciki a Burundi, bayan da aka gano wani babban rami da aka bizne daruruwan mutane da kuma cin zarafin mata.

https://p.dw.com/p/1HeEO
Hoto: Getty Images

Bannan jami'in kula da harkokin kare hakin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad Al Hussein, ya ce dukkannin alamomi dai a yanzu sun nunar cewa akwai yuyuwar kaiwa ga babban tashin hankali tsakanin kabilu a kasar, inda ya ce harkokin tsaron kasar ta Burundi na daf da rugujewa.

Kasar ta Burundi dai, ta fada cikin wannan hali na rishin tabbas tun daga karshen watan Afirilu na bara, bayan da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a wani sabon wa'adi da 'yan adawar kasar da ma sauran kasashen duniya suka kira shi haramtacce.