Kara matakan tsaro a Jamus | Labarai | DW | 03.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kara matakan tsaro a Jamus

Masu nazari a harkokin tsaro a kasar ta Jamus ya ce akwai bukatar sanya idanu sosSai kan masu kaifin kishin addinin Islama da masu kin jinin baki a kasar.

Deutschland Polizei Festnahme in Alsdorf bei Aachen

Jami'an 'yan sanda kan aiki a Jamus

Babban jami'i da ke lura da harkokin tsaron ciki a kasar Jamus ya bayyana cewar akwai bukatar karin kayan aiki a harkokin da suka shafi binciken asiri saboda barazanar masu tsatsauran kishin addinin Islama da ma masu tsananin kyamar baki a kasar.

Hans-Gay-org Maas-sen ya fada wa taron kwararru a fannin tsaro a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus cewa kasar na fiskantar barazana ta ayyukan 'yan ta'adda.

Ya ce mahukunta a kasar na karbar sakonni a kowace rana na shirye-shirye da wasu 'yan ta'addar ke yi. Dan haka sai ya bukaci kara tsaurara sanya idanu kan masu tsaurin kishin addinin Islama da aka kama da wasu laifuka da ma bukatar sanya wasu na'urori da za su rika bibiyar lamuransu.