Kara kulla dangantaka tsakanin Jamus da Russia
October 15, 2007Talla
Shugaba Angela Merkel ta Jamus da takwaran ta na Russia, Vladimir Putin sun fara wani taro na kwanaki biyu a Wiesbaden dake yammacin Jamus. Ana dai sa ran tattaunawar shugabannin biyu zata mayar da hankaline kann kasuwanci da kuma inganta dangantaka a tsakanin kasashen biyu. Bugu da kari taron zai kuma tabo batun rikicin nukiliyar kasar Iran, kana a hannu daya da matsayin yankin Sabiya na kasar Kosovo. Kafin dai tashin Mr Putin zuwa Jamus, rahotanni sun ce an shirya kai masa hari a Iran da nufin halaka shi, a lokacin ziyarar daya shirya kaiwa a cikin wannan mako.Tuni dai mahukunta a Iran suka karyata wannan zargi da cewa bashi da tushe balle makama.