1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

280710 Türkei EU

July 28, 2010

Har yau dai ana famar kai ruwa rana a game da amincewa da Turkiyya a matsayin cikakkiyar wakiliya a Ƙungiyar Tarayyar Turai

https://p.dw.com/p/OWuz
Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle A Turkiyya

A yau ne ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle ke kai ziyara a ƙasar Turkiyya. To sai dai wannan ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ƙasashen Ƙungiyar Tarayar Turai, in banda Birtaniya ke nuna adawa da ƙarbar ƙasar ta Turkiyya a wannan ƙungiya.

Akasarin ƙasashen ƙungiyar Tarayar Turai na kallon ƙasar Turkiya a matsayin babbar ƙasa da ke fama da talauci, take kuma da manufofi masu sarƙaƙƙiya. Kasar ta Turkiya ƙasa ce da ta fi Faransa girma da kuma yawan alumanta yayi kusan daidai da na Jamus. Turkiya ƙasa ce fama da matsalar talauci fiye da ma ƙasar Romaniya. Ba kasafai ne ƙungiyar Tarayar Turai ke magana a bainar jama'a game da kallon da a ke wa Turkiya a matsayin baƙuwa mai aladu daban da za ta haɗe da wata ƙungiya da aladunta suka sha banban da nata ba. Bayan da shugaba Barack Obama ya tunasar game da bukatar haɗe Turkiyya da ƙungiyar Tarayyar Turai a wani taro da ya gudana a birnin Prag na ƙasar Cek shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi wata magana kamar haka:

"A ganina duk wata dangantkar kut da kut tsakanin Ƙungiyar Tarayyar Turai da ƙasashen musulmi musamman Turkiyya wani abu ne da zai biya bukatunmu mu duka ga baki ɗaya. To sai dai har yanzu muna nazari akan yin aiki tare ko kuma karɓarta a matsayin cikakkiyar mamba domin biyan bukata".

Kai tsaye ne dai shugaba Nikolas Sarkozy ya bayyanar da adwarsa da haka:

"A nawa ra'ayin dai Turkiya ba ta da matsuguni a ƙungiyar Tarayyar Turai. Wannan itace abu daya da ba zan canja raayi na a kai ba".

To sai dai kuma Angela Merkel da Nikolas Sarkozy ba su da hurumin canja shawarar da Kungiyar Tarayar Turai ta tsayar game da wannan batu a hukumance. A dai shekarar 2004 ne shugabannin kasashen suka tsayar da shawara gudanar da tattaunawa game da wannan batu. Shekaru 10 zuwa 15 bayan fara tattaunawar ne kuma za a duba irin ci gaban da Turkiyyar ta samu da kuma yiwuwar hadeta da kungiyar Tarayar Turai.

A dai shekaru biyar da suka gabata ƙungiyar ta karɓi sabbin mambobi 12. Samun daidaituwa tsakanin ƙasashen mambobin ƙungiyar guda 27 abu ne da ke bukatar iko da kuma kuɗi . Saboda haka da wuya ƙungiyar ta jiye wa duk wata shawarar ta karɓar wata ƙasa daban kamar dai yadda sabon fraministan Birtaniya David Cameron ya bukata a jiya Litinin yayin saduwarsa da 'yan kasuwa a kasar ta Turkiyya:

"A duk sanda na yi tunane game da irin rawar da Turkiya ta taka a aikin rundunar NATO domin tsaron nahiyar Turai da kuma rawar da take takawa a yanzu a kasar Afganistan. ni kan ji takaicin yadda ake jan kafa wajen karbarta a matsayin mamba ta ƙungiyar Tarayar Turai".

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmad Tijani Lawal