1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kanfanin Deutsche Bahn ya sake yin tayin albashi

November 21, 2007
https://p.dw.com/p/CPrx

Kanfanin jiragen sama na nan Jamus Deutsche Bahn ya sake miƙa tayin sabon tsarin albashi ga direbobin jiragen kasa,yayinda ɓangarorin biyu suka koma teburin tattaunawa da nufin kawo ƙarshen rikicin wata guda tsakaninsu.Sai dai kuma babu wani cikkaken bayani game da tattaunawar tsakanin shugaban kanfanin Harmut Mehdorn da shugaban ƙungiyar direbobin jiragen Manfred Schell.Jerin yajin aiki na tsawon saoi 62 ya janyo ruɗani a harkokin zirga zirgan jiragen haka zalika Jamus tayi hasarar aƙalla euro miliyan 75 sakamakon yajin aikin.Ƙungiyar ta direbobi dai ta bukaci ƙarin kashi 31 cikin dari na albashin ma’aikatanta.