1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kanada zata biya diyyar miliyoyin dala ga wani dan kasar

Gwamnatin Kanada ta amince ta biya diyyar Euro kimanin miliyan 7 ga wani dan kasar amma mai asali da kasar Syria, bayan an kuskure zargin sa da aikata ta´addanci. Mutumin mai suna Maher Arar ya shafe shekara guda a gidan kurkuku na Syria, inda ya ce an gana masa azaba bayan an kore shi daga Amirka a shekara ta 2002. An kame shi ne a filin jirgin sama na John F Kennedy dake birnin New York lokacin da yake kan hanyar komawa gida Kanada bayan wani hutu tare da iyalin sa. FM Kanada Stephen Harper ya fito fili ya nemi gafara daga Arar. Ko da yake ya amince da haka, amma ya ce an jefa rayuwar sa cikin mawuyacin hali.