1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kanada da Australiya sun rufe ofisoshin jakadancinsu a Amman

January 8, 2006
https://p.dw.com/p/BvDC

Kasashen Kanada da Australiya sun rufe ofisoshin jakadancinsu a Jordan na wucin gadi saboda dalilai na tsaron da ba´a bayyana su ba. Wannan dai ya zo ne kwana guda bayan da Birtaniya ta rufe ofishin jakadancinta dake birnin Amman saboda irin wadannan dalilan. Wannan matakin ya zo ne watanni biyu bayan wasu hare haren bama bamai guda uku da aka kai kan wasu otel-otel a Amman wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 50. Kungiyar al-Qaida a Iraqi karkashin jagorancin dan Jordan Abu Musab al-Zarqawi ta yi ikirarin kai hare haren. Australiya da Birtaniya ka iya zama wadanda za´a kaiwa hare-haren saboda goyon bayan da suka ba Amirka lokacin da ta mamaye Iraqi kusan shekaru 3 da suka wuce. Ko da yake Kanada ba ta goyi bayan wannan yaki ba, amma tana marawa gwamnatin Iraqi mai samun daurin gindin Amirka.