Kammala taron SADC Tanzania | Labarai | DW | 29.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kammala taron SADC Tanzania

Shugabannin kasashen kudancin Afrika dake gudanar da taro a birnin Darusalam din kasar Tanzania sunyi kira ga shugaban kasar Afrika ta kudu thabo Mbeki,daya shiga tsakani wajen warware rikicin siyasa dana tattalin arziki a kasar Zimbabwe.A karshen taronsu na yini biyu shugabannin kungiyar kasashen raya kudancin Afrikan,sun kuma yi kira zuwaga kasashen ketare dasu dage takunkumin da suka dorawa kasar ta Zimbabwe.Wannan zartarwar shugabannin dai yazo yini guda bayan ,da jamian yan sandan kasar ta Zimbabwe suka kai somame headquatar jammiyyar yan adawa ta MDC ,inda suka cafke shugaban jammiyar Morgan Tsvangirai da wasu manyan jamiansa.A farkon wannan wata ne kuma jamian yansanda suka tsare yan adawan,inda sukayi musu dukar fitar arziki,data kai su ga jinya a asibiti