1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kammala taron makoki na 'yan Shi'a a Karbala

Gazali Abdou TasawaDecember 3, 2015

Miliyoyin Musulmai mabiya tafarkin Shi'a sun gudanar da taron ranar karshe ta zaman makoki na tunawa da kisan Sayyidina Husseini jikan Annabi Muhammadu a garin Karbala na kasar Iraki

https://p.dw.com/p/1HGn2
Bildergalerie Gesellschaft in Iran
Hoto: AFP/Getty Images

Miliyoyin Musulmai mabiya tafarkin Shi'a sun gudanar da taron makoki na tunawa da ranar da aka yi wa Sayyidina Huseini kisan gilla a birnin Karbala'a. Wannan taron makoki wanda mabiya mazahabin shi'ar ke gudanarwa a ranar cikon kwanaki 40 na zaman makokin shi ne taro mafi girma da muhimmanci ga mabiya wannan tafarki.

Sanye cikin bakaken tufafi mabiya mazahabin shi'ar na dakar kawunansu ko kirjinsu tare da yi wa kansu rauni a kan hanyarsu ta zuwa hubbaran Sayyidina Huseini jikan Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi.

A shekara ta 680 ne dai dakaran halifan daular Banu Umayya wato Yazidu dan Ma'auya suka hallaka Imam Husseini da wasu na kusa da shi a garin Karbala'a a cikin wani kazamin fada.

Kimanin mutane miliyon 20 ne dai suka ziyarci kabarin Imam Huseini din a tsawon wadannan kwanaki 40 na zaman makoki.