Kammala taron kasashen Larabawa | Siyasa | DW | 30.03.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kammala taron kasashen Larabawa

Shugabannin ƙasashen Larabawa sun jaddada bukatar warware matsalar siyasar Lebanon

default

Taron ƙasashen Larabawa a Damascus,Syria.

An kammala taron yini biyu na shugabannin ƙasashen Larabawa a Syria tare da kira ga Lebanon data cimma matsaya guda na warware matsalar siyasa,domin zaɓen shugaban ƙasar. Taron na Damaskus wanda rabin wakilan kungiyar ƙasashen larabawa 22 ne kadai suka halarta ,ya jaddada bukatar dukkannin shugabannin yankin su cimma manufofinsu na ganin cewar an kawo karshen rikicin siyasan dake addabar Syria. Kazalika sun kuma nemi magabatan Lebanon din dasu cimma matsaya guda wajen tabbatar da nadin ɗan takar General Michel Sleiman kamar yadda suka tsara ,akarkashin gwamnatin haɗin kan ƙasa. Mafi yawa daga cikin wakilan ƙungiyar da basu halarci taron badai na zargin Syria da halin da ake ciki yanzu a kasar ta Lebanon. Yanzu tsawon watanni huɗu kena Lebanon bata da shugaban kasa,da karewar wa'adin tsohon shugaba Emile Lahoud a watan Nuwamba.Rikicin dai nada nasaba da sabanin ra'ayin dake tsakanin 'Yan majalisar dokoki dake da goyon bayan ƙasashen yammaci na turai,a hannu guda kuma da 'yan Hizbollahi masu adawa dake samun goyon bayan Iran da Syria. Mai masaukin baƙin taron ƙasashen larabawan shugaba Bashar al-Assad na Syria,wanda kuma ake yawaita danganta rikicin Lebanon din da gwamnatin sa ya bayyana cewar wannan batu ne na cikin gida. "An jima ana zargin mu da halin da ake ciki a Lebanon.Ayayinda wannan batu na cikin gida daya shafi al'ummomin wannan kasa.Muna darajawa kasar kasancewar tana da 'yancin ta da irin tsarin mulkin ta bisa ga doka" Majalisar dokokin Lebanon din dai ta cimma ajiye ranar 22 ga watan Afrilu a matsayin na zaɓen shugaban ƙasar ,bayan ɗagewa har sau 17.Shugaba Assad yayi amfani da kalamai na diplomasiyya adangane da rikicin siyasan na Lebanon.Sai dai shugaba Mammar Gaddafi na Libya yace dole ne kasashen larabawan su rungumi juna idana ana muradin cimma wani cigaba wajen warware matsalolin. "Babu shakka wannan sabani dake tsakanin mu bazai taimaka mana ba.Muna zargi tare da haɗin baki a kan junanmu.Muna neman gazawan junammu.Bayan kamata yayi amatsayimmu na larabawa mu rungumi juna,domin kalubalantar makiyammu" Taron dai ya aike da sako gargadi na musamman zuwa ga Izraela,nacewa larabawan na nazarin janye tayin sulhu da sukayi mata idan har bata sauya halin ta ba Shugaba Assad na Syria dai yace Izraela akarkashin jagorancin Ehud Olmert,batutuwan cimma zaman lafiya na fuskantar tafiyar hawainiya.. "Ana cimma zaman lafiya ne ta hanyar bada 'yancin walwala wa mutane,amma ba ta hanyar tursasawa da yaki ba.Babu yadda za a cimma zaman lafiya idan baa bawa mutane 'yancin su ba". A karkashin wannan shirin dai ƙasashen larabawan sun jaddada bukatar aiwatar da daftarin ,wanda shine hanyar warware rikicin dake tsakanin Izraela da ƙasashen.