Kamitin Sulhu ya gaza cim ma daidaito kan batun Iran.
May 10, 2006Talla
Ministocin harkokin waje na ƙasashe masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da na Jamus, sun gaza cim ma madafa kan batun zartad da ƙuduri game da rikicin da ake yi kan shhirye-shiryen makamashin nukiliyan Iran. Yayin da Birtaniya da Faransa da Amirka ke fafutukar neman a sanya wa Iran ɗin takunkumi ko ma ɗaukan soji a kanta, idan ba ta dakatad da ayyukan inganta yureniyum da take yi ba, ƙasashen Sin da Rasha na adawa da wannan yunƙurin.
Ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier, wanda shhi ma ke halartar taron ministocin a birnin New York, ya ce har ila yau da akwai wasu maganganu guda 6 da ba a warware su ba tukuna, kuma za a bukaci har tsawon mako biyu kafin a iya cim ma yarjejeniya.