1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfanonin Siemens da na Alstom za su hade

Gazali Abdou Tasawa MNA
September 27, 2017

Mahukuntan kasashen Jamus da na Faransa na nazari kan shirin hadewar kamfanin Alstom na Faransa da kuma Siemens na Jamus a wuri daya domin tafiyar da ayyukansu na harkokin jiragen kasa a tare.

https://p.dw.com/p/2kmDD
ICE und TGV
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Murat

Kamfanin Alstom na Faransa da kuma Siemens na Jamus sun ba da sanarwar hadewa wuri daya domin tafiyar da ayyukansu na harkokin jiragen kasa a tare. Hadakar kamfanonin biyu za ta haifar da sabon kamfani mai suna Siemens Alstom wanda kuma zai kasance na biyu a duniya a fannin harkokin jiragen kasa. 

Idan har wannan shiri ya tabbata shaharraren jirgin kasar nan mai gudun fanfalaki wato TGV kirar Faransa zai koma mallakar kasashen biyu. Sai dai yarjejeniyar ta tanadi cewa kamfanin Siemens na Jamus shi ne zai mallaki kashi 50.5% cikin 100 na hannun jarin kamfanin nan da shekaru hudu masu zuwa. 

Da yake jawabi a gaban majalisar dokokin Faransa kan wannan shiri karamin ministan kudi na kasar Faransa Benjamin Griveaux  ya ce shirin kasashen biyu na da nufin fuskantar da barazanar da suke fuskanta daga kamfanin CRRC na Chaina a fannin wannan sana'a, inda ya yi karin bayani yana mai cewa:

"Yanzu kamfanin CRRC na Chaina ya fi karfin kamfanonin Alstom da Siemens da Bombardier na Kanada idan aka hadesu wuri daya, don haka burin kamfanin Chainar a nan gaba shi ne mamaye Turai."