Kamfanonin daukar ma´aikata haya a Jamus | Zamantakewa | DW | 29.04.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Kamfanonin daukar ma´aikata haya a Jamus

Bayani kan tsarin daukar ma´aika haya a Jamus

default

Leburori a bakin aiki

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Mu Kewaya Turai, shirin da ke kawo muku batutuwan da suka shafi siyasa, tattalin arziki, al´adu, zamantakewa da kuma dangantaka tsakanin ƙasashen nahiyar Turai.

Yanzu dai abin da yafi ciwa Jamusawa musamman masu neman aiki, tuwo a ƙwarya shi ne irin kamfanonin na masu ba da hayar ma´aikata, waɗanda ke ci da gumin marasa aikin yi da ke neman aiki ruwa a jallo. Yanzu dai a nan Jamus alƙalumma sun yi nuni da cewa mutane kimanin dubu 600 ne ke aiki ƙarƙashin kwantaragi na kamfanoni masu ba da hayar ma´aikata. Ana ɗaukar hayar ma´aikata ne don cike giɓin ƙarancin ma´aikata a kamfanoni ko kuma lokacin da ayyuka suka yiwa kamfani yawa ta yadda a dole sai ya ɗauki ƙarin ma´aikata musamman na wucin gadi. Wannan dai shi ne maƙasudin ƙirƙiro kamfanonin ba da hayar leburori. To sai dai a yanzu ana yawaitar sauƙaƙa dokokin ƙirƙiro da kamfanonin. A halin nan da ake ciki kamfanoni da yawa na amfani da ma´aikatar haya ne domin samun leburori masu araha. To a cikin shirin na yau zamu duba wannan batu ne na ma´aikatan haya da kuma masu ɗaukarsu aiki. Masu sauraro Mohammad Nasiru Auwal da ATB ke marhabin da saduwa da ku a ciki shirin.

Bisa al´ada a duk lokacin da ya koma gida bayan ya tashi aiki Patrick Brettschneider dake zaune a wani ƙaramin gari dake kusa da birnin Leipzig dake gabashin nan Jamus, ya kan huta kan wata kujera yana duban waje daga tagarsa yana shan shayi kuma ya na busa taba sigari. Patrick ya yi bayanin aikin sa yana mai cewa.

Brettschneider:

“Ina aiki ne a wata masana´antar dafa giya. Ina aiki daidai kamar sauran ma´aikatan da masana´antar ce da kanta ta ɗauke su aiki wato ba waɗanda kamfanin ba da hayar ma´aikata ya sama musu aiki ba. Ni na ke kula da shara da kuma tsabatar masana´antar.”

Tun kimanin shekaru biyu da suka gabata wannan leburan haya ɗan shekaru 31 da haihuwa ya ke wannan aiki. A wancan lokaci dai ya kasance mai neman aiki ruwa a jallo, amma sai ya ga cewa ba zai samu aiki kai tsaye ko da na wucin gadi ne a wani kamfani ba. Saboda haka ya nemi taimakon kamfanin ba da hayar ma´aikata, wanda a cikin ƙanƙanin lokaci ya samu masa aiki a wannan masana´anta ta dafa giya, inda yanzu haka ya shafe shekaru biyu yana aiki. Ya yi nuni da cewa kimanin kashi 60 cikin 100 na ma´aikata a wannan masana´anta, ´yan haya ne.

Brettschneider:

“Abin da ke ci min tuwo a ƙwarya shi ne ana yi mana kallon ma´aikata masu daraja ta biyu. A gaskiya bai kamata a ce an samu wani bambamci ko nuna fifiko a tsakanin ma´aikata irin mu waɗanda aikin su bai wuce irin na lebura ba. To amma abin baƙin ciki yanayin da muke ciki ke nan saboda kasancewarmu ma´aikatan haya.”

Albashin Brettschneider kamar na sauran leburorin haya, bai taka kara ya karya ba. Kamfanin hayar ma´aikatan ne ke biyan shi albashin wanda bai wuce Euro 6 da Cent 50 a awa ɗaya ba. Bayan an zabtare kuɗin haraji abin da ke saura a matsayin albashinsa na wata bai kai Euro dubu ɗaya ba, wato kwatankwacin rabin albashin cikakken ma´aikaci na wannan masana´anta.

Brettschneider:

“A ƙarshe wannan wani albashi ne kawai na jefa ma´aikaci cikin yunwa. Ba yadda zaka iya ciyar da iyalinka da wannan albashi na ƙasƙanci da ci da gumin marasa galihu.”

A halin nan da ake ciki ana yawaita bukatar ma´aikatan haya. Ba don kome ba sai saboda kamfanoni na son ma´aikacin da zasu iya sarrafa shi yadda suke so. Yanzu haka kashi ɗaya bisa shida na ma´aikata a Jamus na samun aiki ne ta kamfanonin ba da hayar ma´aikata. Hans-Ulrich Brautsch na cibiyar nazarin tattalin arziki dake birni Halle ya yi bayani yana mai cewa.

Brautsch:

“Kamfanoni na amfani da ma´aikatan haya don cike giɓin da ake samu a lokacin da aiki yayi yawa ko suke fama da ƙarancin ma´aikata. Wato su na bukatar ƙarin ma´aikata na wucin gadi.”

Hatta a reshen kamfanin ƙera motoci na BMW dake birnin Leipzig, ma´aikatan haya na taka muhimmiyar rawa a ayyukan kamfanin. Yanzu haka dai kamfanin ya ɗauki ma´aikata dubu ɗaya a matsayin na wucin gadi. Kakakin BMW a Leipzig Michael Janssen ya ce ma´aikatan haya sun kai kashi ɗaya bisa uku na ilahirin ma´aikatansa.

Janssen:

“A matsayinmu na kamfani muna cikin wata gogayya. Babban burinmu shi ne kamfaninmu ya ci-gaba a matsayin mai zaman kansa. Wato kenan dole mu ci-gaba da samar da kayayyaki masu inganci a cikin wannan gogayya. Muna cikin wani hali na tsaka mai wuya a dangane da kuɗin da muke kashewa na samar da kayaki. Shi yasa dole mu ɗauki matakan tsimi domin mu ci-gaba da zama cikin wannan gogayya.”

Nan gaba kamfanin BMW dai na son ya ƙera yawan motoci da yake yi a yanzu amma da ma´aikata kaɗan. Dole kuwa sai tare da ma´aikatan haya sannan kamfanin zai cimma wannan buri na sa. Idan ba haka ba to dole kamfanin ya nemi sabon wuri wataƙila a ƙasar waje inji Janssen.

Janssen:

“Kamfanin BMW yana da ma´aikata kimanin dubu 76 a nan Jamus. Yana da manyan rassan huɗu na ƙera motoci da babura. Kana yana da wata cibiyar bincike da dubban ma´aikata. Ba zamu iya tafiyar da aikinmu a Jamus ba sai tare da wannan tsari na ma´aikatan haya ba.”

A dangane da haka tsarin ma´aikatan haya ke ƙaruwa a Jamus wanda hakan ke haddasa ƙaruwar leburorin haya a cikin ƙasar. Duk wanda Allah Ya ɗigawa garinsa madara, yana samun aikin dindindin kai tsaye a kamfanin da yake yiwa aiki. To amma Patrick Brettschneider ba zai samu wannan sa´a ba. Hasali ma yanzu ya yanke ƙaunar samun wani aiki na cikakken kwantaragi.

Brettschneider:

“A wannan yankin da muke ciki ba wani kamfani da zai ɗauki wani lebura aiki kai tsaye. Komai na tafiya ne ta hannu kamfanonin hayar ma´aikata.”

A saboda haka Patrick Brettschneider ya ce zai bar wannan yankin. Ya ce da zarar ya samu wani aiki na dindindin, bai ga abin da zai riƙe shi a Leipzig ba.