Kamfanin Daimler tarmamuwar Apartheid ? | Siyasa | DW | 15.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kamfanin Daimler tarmamuwar Apartheid ?

Wasu Ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin jama´a a Afirka ta Kudu na zargin kamfanin Daimler da taka muhimmiyar rawa a wanzuwar mulkin wariyar launin fata.

default

An zargi Kamfanin Daimler da taka rawa a mulkin Apartheid

"Tarmamuwar mulkin wariyar launin fata", wannan shine, jigon wata gagaramar kampe da masu radin yaƙi da Apartheid suka ƙaddamar a Afrika ta Kudu, da zumar samun haɗin kan mutanen ƙasar,domin  su danganta kamfanin ƙira motocin Jamus na Daimler a matsayin kamfanin da ya taka muhimmiwar rawa wajen wanzuwar mulkin wariyar launin fata.

Mutanen da suka ƙaddamar da wannan kampe, na zargin kamfanin Daimler da kasancewa uwa makarɓiyar, a mulkin wariyar launin fatar da ya wakana  a ƙasar Afrika ta Kudu.A cewar su ,kamfanin, mallakar ƙasar Jamus, shine ya samar da motoci ga jami´na tsaron ƙasar, wanda suka  yi amfani da su domin hallaka dubun- dubatar jama´a .

Sun yi suka da kakkausar halshe ga kamfanin a  game da abinda suka kira take haƙƙoƙin bani adama.

Wannan jerin zarge-zarge sun zo a daidai lokacin da Daimler ya tsinci kansa cikin wani mayucin hali.

A shekara da ta gabata, ya samu asarar da ta bai taɓa yin irin ta ba, sannan ya tsinci kansa cikin wani yanayi na cin hanci da karɓar rashawa, abinda ya jawo masa biyan tarar dallar Amurika milion 185.A wani babban taro da masu hannun jari a cikin kamfanin suka shirya jiya a birnin Berlin ,shugaban Daimler, Dieter Zetsche, yayi nadama game da wannan hali da kamfanin ya shiga, tare kuma da yin alƙawarin ɗaukar matakan da suka dace:

"Mun gane kura-kurenmu, kuma zamu gyarawa saboda mutunci da darajar kamfanin".

Masu radin yaƙi da mulkin wariyar launin fata a Afrika ta Kudu, sun bukaci gyaran wannan kura-kurai ya haɗa da biyan diyya ga asara dubunan rayuka da kamfanin Daimler ya haddasa a ƙasar lokacin mulkin Apartheid.

Binciken da suka gudanar ya gano cewar, wannan kamfani shine ke samar da makamai da motocin yaƙi wanda gwamnatin Apartheid tayi amfani da su.A cewar Mpho Masemola na Ƙungiyar kare haƙƙoƙin jama´a ta Khulami dake Afrika ta Kudu , Daimaler ya samar da motoci aƙalla 2.500 ga gwamnatin wariyar launin fata.

" Duk da cewar diyya ba zata taɓa biyan asara rai ba , amma muna buƙatar kamfanin Daimler ya biya diyya ga magadan da gwamnatin  Apartheid ya hallaka ta hanyar amfani da makamai da motocin da kamfanin ya sayarwa Afrika ta Kudu.

Bayan asara rayuka an nyi asara gidaje mai yawa, mutane da dama suka sami kansu ba matsugunni".

Shi da kansa Masemola  yana ɗaya daga jerin mutanen da suka dandana kudar su  a lokacin mulkin Apartheid domin shekara biyar ɗaure kurkuku kuwa ya samu rauni bayan da wani ɗan sanda ya harbe shi.Yau shekaru takwas da suka gabata, ya haɗa kai da wasu mutanen da suka sha azaba a lokacin, domin shigar da ƙara a wata kotun Amurika.Bayan kotu ta yi watsi da ƙarar amma yau da shekaru ukku kuma ta fara bincike akai.

A lokacin zaman taron da masu hannun jarin kamfanin Daimler suka shirya, sun ambato batun shigar da ƙaran, kuma suna jiran sakamakon da kotun zata bayar.

A ɗaya wajen, Daimler ya yanke shawara katse hulɗoɗi da wani kamfanin kasar Iran, matakin da Ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani adama suka yi lale marhabin da shi. To saidai game da batun Afrika ta Kudu, Daimler yayi tsayuwar gwamanen jaki, tare da yin watsi da bukatar biyan diyya.

Mawwallafi:Yahouza Sadissou Madobi Edita: Umaru Aliyu