1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Takun sakar gwamnati da 'yan aware

Ahmed Salisu
March 13, 2018

Yayin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin mahukuntan Kamaru da 'yan awaren Ambazoniya rahotannin da ke fitowa daga kasar na nuni da yadda mutane ke bacewa cikin wani yanayi mai daure kai.

https://p.dw.com/p/2uEuh
Kamerun Soldaten Anti Boko Haram
Hoto: picture-alliance/dpa/N. Chimtom

Bacewar Aaron Animbom ta tada hankalin mahukuntan Yawunde musamman ma dai bayan da wani bidiyo da ke dauke da hotonsa ya bayyana inda a cikinsa wadanda ke rike da shi suka ce su mambobi na rundunar sojin Ambazonia kuma suka ce suna rike da Mr. Animbom a wani mataki na matsin lamba ga gwamnatin kasar kan ta sako shugabansu Atuk Tabe da wasu mutane 46 da aka kama a Najeriya kana aka iza keyarsu zuwa Kamaru.

A cikin faifan bidiyon da suka fidda dai, Mr. Animbom da ya bayyana cikin tufafin da ke a dukunkune kana ya nemi gwamnatin Paul Biya wadda ya ke yi wa aiki a kan ta gaggauta biyan bukatar dakarun na Ambazonia saboda su sake shi kafin su kai ga hallaka shi kamar yadda suka yi ikirari.

Shi dai Mr. Animbom ya gamu da wannan wadanda suka yi awon gaba da shi ne lokacin da ya koma gida bayan ya halarci jana'izar wani jami'in gwamniti mai suna Joseph Namata wanda aka kama a gidansa a garin na Batibo da ke arewacin kasar. Tun cikin watan Janairun da ya gabata ne dai bangaren arewacin Kamaru da ke amfani da harshen Turancin Ingilishi ya sake tsunduma cikin wani yanayi na tashin hankali, biyo bayan kame jagororin Ambazonia da aka yi batun da ya sanya suka shiga afkawa jami'an tsaro da kame manyan ma'aikatan gwamnati saboda yin garkuwa da su. Daruruwan mutane ciki har da sojoji da 'yan sanda 30 ne dai suka hallaka sakamakon wannan tashin hankali.