Kamaru: Kotu ta dage shari′ar ′yan gwagwarya | Labarai | DW | 14.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamaru: Kotu ta dage shari'ar 'yan gwagwarya

A wannan Litinin wata kotu a birnin Yaounde na kasar Kamaru ta dage shari'ar 'yan gwagwarmayar nan na yankin da ake magana da harshen Ingilishi da ake tuhuma da laifin ta'addanci.

Jim kadan ne dai bayan da kotun ta zauna, sai kuma ta dage wannan zama har ya zuwa ranar 23 ga watan Maris. Mutanen uku dai sun hada da Félix Agbor Nkongho, wani lauya, da Neba Fontem Aforteka'a malamin makaranta, da kuma Mancho Bibixy wani ma'aikacin rediyo da ake kira da sunan BBC, an kamasu ne a watan Janairu da ya gabata. Lauyoyi fiye da 160 ne dai suka hadu domin basu kariya.

Ana zargin mutanen uku ne dai da laifin tunzura jama'a, da neman a raba kasar biyu, da neman tada zaune tsaye, da kira zuwa ga yaki kamar yadda aka rubuta a kundin tuhumar da ake yi musu. Sai dai tun a zama na farko mutanen uku sun ki amsa laifin da ake zarginsu da shi.