1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Hukunci kan masu tada bore

March 23, 2017

Hankula sun tashi a Kamaru a dai dai lokacin da ake shirin yanke hukunci kan wasu da suka yi kiran yajin aiki bangaren kasar mai amfani da turancin Ingilishi.

https://p.dw.com/p/2Zo8g
Nigeria Demonstration 8. Februar 2015
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Kouam

Shugabannin su uku, na iya fuskantar hukuncin kisa muddin aka same su da laifi kan zargin da ake masu na kiran bangaren da su balle daga kasar. 

Zaman kotun sojin kasar a yau Alhamis, zai dauki mataki kan jagororin 3 ne, yayin dubban jama'a da ke goyon bayansu a yankin arewa da kuma kudu maso yammacin kasar ke kiran da a gaggauta sakinsu ba tare da wani sharadi ba.

Mutanen wadanda ke yanki mai amfani da harshen Inglishi na cewa ne sakin jagororin ne kawai zai tabbatar da dawowar harkokin karatu dama sana'o'in da aka rufe kimanin watanni hudu yanzu.

Ga alama dai yajin aikin wanda ya haddasa girman rigimar, zai ci gaba.

 

Wakilan bangaren Kamaru mai amfani da Ingilishi ne a majalisa ke nuna turjiya ga sake nadin Cavaye Yegae Djibril, a matsayin kakakin majalisar wanda kuwa dan bangaren kasar mai amfani da faransanci ne.

Dan majlisa Joseph Mbah Ndam ya ce bangaren masu rinjayen kasar na jam'iyyar CPDM, sun gaza basu ko da matsayi na mataimakin kakaki a majalisar, wanda ya sanya ala tilas, su ke korafi.

 

Ya ce "mun gabatar da kwaskwarima kan dokar da zai baiwa bangren kasar matsayin  mataimakin kakaki, idan kakaki ya kasance daga bangaren masu amfani da harshen faransanci.

Kamerun Präsident Paul Biya
Shugaba Paul Biya na KamaruHoto: imago/Xinhua Afrika

 

Wannan dai kadan ne daga irin tada jijiyoyin wuya da ta kasance kasar Kamaru tun cikin watan Nuwamban bara.

Lauyoyi da malamain yankin masu amfani da Ingilishin sun shiga wani yajin aiki ne sai illa-masha-Allahu saboda abin da suke ce fifita faranci da ake yi a fadin kasar.

Yajin aikin dai ya haddasa kame-kame da kone-konen makarantu da asibitoci da ofisoshin jami'an ‘yan sanda da wasu ma'aikatu dama kasuwanni.

An dai zargi sojojin kasar da aka aika don kwantar da rigimar da take hakkin masu zanga-zangar gami da yiwa mata fyade.

Daga cikin wadanda za su gurfana a kotun nay au dai hard a, mataimakin babban lauyan gwamnati Ayah Paul.

Gwamnatin ta yi zargin cewar an kona tutocin kasar lokacin gangamin tare da dasa wasu da aka ce na sabuwar kasa ce mai cikakken iko.

Maatsalar ta mayar da harkokin ilimi baya matuka, ganin cewa an ma kaiga rufe jarrabawar karshe, kashi 40 ne cikin dalibai dubu 200 na yankin masu amfani da Ingilishi suka yi rajista.

Wasu dalibai ma sun koma wasu makarantun da ke sauran bangarorin kasar.

Kamerun Mokolo Markt in Yaounde
Zanga- zanga a yankin da ake magana da IngilishiHoto: Getty Images/AFP/R. Kaze

 

Wani dan siyasa Mbella Moki Charles, y ace matsalar na dada ta'azzara ne saboda ci gaba  da tsare shugannin da aka yi bayan bukatar hakan da jama'a suka nunar.

Dole ne fa mu fadi gaskiya. Mutane na cewa an koma makarantu, babu wata makarnatr da ke aiki. Yanzu idan kana da yara 100 da ke zuwa makaranta, 10 zuwa 20 ke zuwa. Ba za yi farin cikin kasancewar akasarin yara babu karatu ba. Zamu baiwa shugaban kasa cikakken bayani don ya warware matsalolin.

Gwamnatin Kamaru dai ta toshe hanyoyin sadarwar internet, saboda zargin matasa da na amfani da kafofin sada zumunta wajen ruruta rikicin.


Wasu mafusatan dai na kiran samar da gwamnati daya da kasa baki daya, yayin da a daya hannun wasu ke nemam ballewa.

Shuagaba Paul Biya na kasar ya gana da shugaban kasar Italiya a wannan makon, inda y ace sun tattauna batun.

Shugaba Paul Biya ke cewa mun yi Magana da shi kan matsalolin shiyoyin. Na kuma tabbatar mishi cewar galibin ‘yan Kamaru na bukatar zaman lafiya da juna duk da bambance bambance. A shirye gwamnati ta ke don tattaunawa, don kada a dora ayar tamabaya kan hadin kan al'umar kasarmu.

Wannan rikicin dai ya kai yanzu ana ganin wasu takardu na hukuma cikin turancin Ingilishi. Haka nan kuma ya ke a wasu ma'aiktun gwamnati kana wasu ma daga cikin jami'an gwamnati sun fara gabatar da jawabai cikin harshen na Ingilishi.