Kamaru: Harin bam a wata kasuwa
February 19, 2016Talla
Wasu tagwayen hare-haren bama-bamai a wata kasuwa a lardin Meme da ke a Arewacin Kamaru ya yi sanadi na rayukan mutane 19, yayin da wasu 50 suka samu raunika kamar yadda mazauna yankin suka bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters.
Wannan dai shi ne hari na baya-bayan nan da ya yi sanadi na rayukan mutane da dama a Arewacin na Kamaru da ke ganin yawaitar ayyukan ta'addanci daga kungiyar Boko Haram mai sansani a Najeriya.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki nauyin wannan kai hari da aka saba ganin kungiyar ta Boko Haram na kaishi.