Kamaru: Cocin Katolika ya yi tsokaci | Labarai | DW | 06.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamaru: Cocin Katolika ya yi tsokaci

Shugabannin Cocin Roman Katolika na yankin da ke magana da harshen Inglishi a Kamaru sun bayyana takaicinsu a game da yadda jami'an tsaro suka yi amfani da makaman gaske wajen murkushe 'yan aware masu neman ballewa.

A cikin wata sanarwa da suka bayyana jami'an Cocin na Bamenda sun ce, 'yan awaren wadanda suka yi yunkurin bayyana sanarwar ballewar a ranar daya ga watan Oktoba ba sa dauke da makamai don haka bai kamata ba sojojin su fatatakesu da bindigogi ba. Sannan kuma sanarwa ta ce wasu jama'ar a ciki har da yara an bindigesu har lahira a lokacin da za su je Coci.