1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

kalubalen tattalin arziki a Zimbabuwe

Abdul-raheem Hassan
September 29, 2017

Mazauna kasar Zimbabuwe na cikin fargabar sake fadawa matsin tattalin arziki. A yanzu dai 'yan kasar na ta hada-hadar sayo kayan abinci dan gudun tsadar kayan masarufi a nan gaba.

https://p.dw.com/p/2kygb
Bildergalerie langjährige Herrscher Robert Mugabe
Hoto: Getty Images/AFP/J. Njikizana

Manya da kananan 'yan kasuwa a kasar Zimbabuwe na ci gaba tsauwalla farashin kayan abinci da sauran kayan masasurufi sai dai masana tattalin arziki na danganta matsalar da rashin wadatar kudaden kasashen waje a hannun al'umma. Chitambara, wani mai fashin baki ne kan harkoki tattalin arziki, ya kuma bayyana hakikanin halin tsadar rayuwa da kasar ke fuskantar kasar inda ya ke cewar  "a yanzu muna fuskantar faduwar darajar kudade lamuni a kan kudaden dalar Amirka a kasuwanin canji, wannan kuma ya haifar da illa ga tsare-tsare. Kamfanoni da dama na goyayya da juna wajen neman kudaden wajen dan yin rige-rigen sayen kaya daga waje."

Tun a watan Afirilun shekara ta 2016 ne dai Zimbabuwe ta kaddamar da amfani da takardun lamuni da nufin saukaka wahalar karancin kudi da ake fama a hadadar kasuwannin kasar. Duk da irin tabbaci da kuma yakinin da gwamnatin kasar ke da ita a kan tsarin takardun lamunin, amma 'yan kasar irin su Faith Rindai na dari-dari da makomar kasar. Faith ta ce "muna ta faman kimsawa dan gudun shiga tsananin azabar yunwa da ka iya kashe mu saboda 'yan kasuwa na ninka farashin kaya. Muna ta tara abinci dan gudun kada su kare a shaguna, muna fargabar abinda ya faru a shekara ta 2008."