Kalubalen tattalin arziki a Najeriya | Siyasa | DW | 09.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kalubalen tattalin arziki a Najeriya

A ci gaba da kokarinsu na kaiwa ga ficewa daga cikin halin masassarar tattalin arziki, gwamnatin Tarrayar Najeriya ta fitar da wani sabon shirin habaka tattalin arzikin kasar a shekaru ukun da ke tafe.

Sabon shirin dai na da burin kai karshen masassarar da tattalin arzkin Najeriyar ke fama da ita da kuma bunkasa tattali na arzikin kasar zuwa digo bakwai cikin 100 kafin nan da shekaru ukun da ke tafe. A banan dai Tarrayar Najeriyar na fata na ficewa daga cikin masassarar tare da samar da ci gaba na kusan sama da digo biyu, karkashin shirin da ke kallon noma da harkar masana'antu a matsayin mafita ga kasar. A cikin shekaru ukun da ke tafen dai Najeriyar na da fatan wadatar da kanta da shinkafa da tumaturi da kuma alkama, a wani matakin da take kallon zai kawo karshen barna ta kudade. Ko bayan nan kasar na kuma burin samar da hasken wutar lantarkin da ya kai Gigawatt 10 domin amfanin masana'antu na kasar, a fadar ministan kasafi da tsare-tsare na tattalin arzikin kasar Udoma Udo Udoma wanda kuma ya ce: "Tarrayar Najeriyar za ta koma mai wadatar da kanta da man fetur maimakon shigo da shi daga kasashe na waje.

Tilasta gwamnati daukar matakan da suka dace.

Sauke darajar naira a Najeriya da nufin habaka tattalin arziki

Sauke darajar naira a Najeriya da nufin habaka tattalin arziki

Duk da cewar dai dole kanwar naki ta sa Najeriyar ta dagewa ga batun samar da abincin, sannan kuma ta fara ganin alamun haske sakamakon rage darajar kudin kasar na naira, babbar matsala har ya zuwa yanzu dai na zaman na rashin haske na wutar lantarkin duk da cefanar da kamfanonin samar da wutar da ta yi, abun kuma da ke zaman karfe na kafa ga kokari na tashin masana'antun da gwamnatin ke kallon zai tasiri wajen rage fatara da samun aiki a tsakanin al'umma. Mallam Abubakar Ali dai na zaman wani masani ga batu na tattali na arzikin, ya kuma ce: "Gwamnatin na iya nasara cikin shirin amma in ta amince zama babbar kasuwa ga kamfanoni na gida maimakon maida hankalinta zuwa waje." To sai dai kuma ko ta ina gwamnatin ke fatan nasarar fitar da wando ta tsakar ka dai, wani abun da ke iya tarnaki ga cimma bukata dai na zaman shirin zabe na kasar nan da tsawo na shekaru biyun da ke tafe, abun kuma da ke iya kautar da hankali na Abujar daga hanyar cika burin tare da kila mai da hannu na agogo baya. Amma a fadar ministan tsara tattalin, zaben zai za mo musu kaimi maimakon tarnaki a burin dora kasar ya zuwa tudun mun tsira. Abun jira a gani dai na zaman tasiri na shirin da ke da burin lamushe dubban miliyoyi na daloli da kuma gwamantin kasar ta dora shi bisa bashi daga kasashen ketare.

 

Sauti da bidiyo akan labarin