1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen dake gaban Jamus a wa´adin shugabancin ta na ƙungiyar EU

Mohammad Nasiru AwalJanuary 3, 2007

Jamus zata ba da fifiko a kan samun maslaha dangane da kundin tsarin mulkin ƙungiyar tarayyar Turai a wa´adin shugabancin ta na wata 6.

https://p.dw.com/p/Btwo
Angela Merkel
Angela MerkelHoto: AP

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka barkan mu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na MKT. Daga ranar daya ga watan janeru Jamus ta karbi shugabancin karba-karba na KTT a watanni 6n farko na wannan shekara ta 2007. A wannan rana ce kuma aka dauki kasashen Romania da Bulgaria a cikin kungiyar. Alal hakika a duk lokacin da wata babbar daula ta Turai ta karbi jagorancin kungiyar, a kan sanya dogon buri don cimma nasarori a batutuwa da dama musamman game da kundin tsarin mulkin kungiyar da ya cije. To shirin na yau zai yi nazari akan kalubale da kuma rawar da SGJ Angela Merkel zata taka a matsayin sabuwar shugabar KTT. Masu sauraro MNA Ke muku lale maraba a cikin shirin.

Madalla. SGJ Angela Merkel, wadda ake yiwa lakabi da mace mai kamar maza a Turai, ta yi nuni da cewa Jamus zata yi amfani da wannan dama a matsayin shugabar KTT don gano bakin zaren warware matsaloli da dama da suka zamewa kungiyar kayar kifi a wuya.

“A gaskiya wa´adin shugabancin kungiyar EU wani lokaci ne na musamman ga ko-wace kasa. Saboda haka mu ma muna murna da wannan lokacin, kuma muna sane da irin aikin dake gaban mu. Jamus zata taka rawar gani.”

Merkel dai na da kyakkyawan fatan cewa zata ceto kundin tsarin mulkin KTT. Jacki Davis masaniyar kimiyyar siyasa a cibiyar tsara manufofin kasashen Turai dake birnin Brussels ta yi tsokaci akan haka.

“Tun bayan da kasashen Holland da Faransa suka yi fatali da kundin tsarin mulkin kungiyar EU aka shiga cikin hali na rashin sanin tabbas. Abin da ya kamata Jamus ta yi shi ne ta samar da wata maslaha karbabbiya ga kowa da kowa. Ko shakka babu Jamus na da jan aiki a gaban ta, musamman bisa sabanin da ake fuskanta tsakanin kasashen dake son ceto kundin tsarin mulki da wadanda ke son a yi watsi da shi gaba daya.”

Jackie Davis ta yi imanin cewa Merkel zata taka rawar gani musamman bayan gudunmawar da ta bayar wajen samun maslaha takaddamar game da kasafin kudin kungiyar EU a bara. Hakan ya kara mata daraja daga dukkan sassan da abin ya shafa ciki har da hukumar EU da majalisar Turai, inji Jacki Davis.

“Ana bukatar kwarewa ta yin shawarwari. Saboda haka ya zama wajibi ta tattauna da takwarorinta na EU don dinke barakar dake tsakani. A nan birnin Brussels ana jin cewa Merkel ta cike dukkan sharuddan da ake bukata, to amma aiki ne mai wahala. A matsayin ta na shugabar EU dole zata yi sara tana duban bakin gatari. Domin ba bukatun EU ne kadai zata duba ba, dole ne kuma ta duba bukatun Jamus.”

Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin wajen Jamus F-W Steinmeier zai kokarin fahimtar da takwarorin sa na sauran kasashe 26 na kungiyar ta EU a yanzu bayan daukar kasashen Romania da Bulgaria, muhimmacin samun maslaha game da kundin tsarin mulklin. A halin da ake ciki kasashe 18 ciki har da Jamus sun amince da kundin kamar yadda ya ke a yanzu, to amma Jamus din kanta ba ta san takameme irin sabbin shawarwarin da zata gabatar bisa manufa ba. A saboda haka Angela Merkel ta yi kashedi game da sanya dogon buri, tana mai cewa.

“Abin da ke akwai shi ne a wa´adin shugabancin na Jamus ba za´a samu wani sakamako ba a kan batun na kundin tsarin mulkin EU. Abin da zamu yi shi ne Jamus zata share fage domin samun sukunin warware wannan takaddama gabanin zaben shugaban kasar Faransa da za´a yi a shekara ta 2008. Za´a kuma fadakar da jama´a game da zaben majalisar dokokin Turai.”

A cikin lokacin bazara na shekara ta 2009 za´a gudanar da zaben na majalisar dokokin Turai, kuma kamata yayi dukkan kasashen EU su rataba hannu kan tsarin mulkin kafin wannan lokaci. Wato kenan dole sai an sake gudanar da kuri´ar raba gardama a kasashen NL, Faransa, Poland da kuma Birtaniya.

A lokacin shugabancin Jamus wato a ranar 25 ga watan maris za´a yi bukin cika shekaru 50 da kafa KTT. Jamus na fatan wannan buki da ya hada da na al´adu da tarukan shugabannin EU zai taimaka wajen daga martabar kungiyar a idanun al´umar Turai. A cikin wata sanarwa da ta ke shirin aikewa dukkan membobi da hukumomin EU, gwamnati a Berlin ta nuna bukatar sake fasalta kungiyar. To amma har yanzu ana kai ruwa rana game da shawarwarin da sanarwa ta kunsa. Ministan harkokin wajen Jamus F-W Steinmeier cewa yayi.

“Zamu ba da wata sanarwa wadda a ciki zamu yi kokarin nuna dalilan da suka sa aka kirkiro kungiyar EU. A namu ganin ba za´a iya canza wadannan dalilai ba. Zamu kuma nuna irin alhakin da ya rataya a wuyan mu da hanyoyin da zamu bi don sauke su.”

Baya ga batun tsarin mulkin, Jamus a matsayin ta na shugaban majalisar zartaswar Turai zata fuskanci jerin kalubale na manufofin ketare na EU, da ya kama tun daga tattaunawar daukar Turkiya da matsayin yankin Kosovo har zuwa manafofinta game da sabbin makwabtanta na yankin tsakiyar Asiya. Benita Ferrero-Waldner kwamishinar ketare ta EU ta ce za´a mayar da hankali ga hadakar wannan yanki mai arzikin makamashi da albarkatun kasa da nahiyar Turai a cikin watanni 6 masu zuwa.

“Ina sa ran samun shugabanci na gari daga Jamus, wadda zamu hada kai tare domin fadada manufofin mu da suka shafi makwabtanmu na yankin tsakiyar Asiya da kuma GTT, don kashe wutar dake barazanar mamaye ilahirin yankin na GTT.”

Tabbacin samun makamashi da kara sakarwa harkokin kasuwancin makamashi mara a Turai zai kasance cikin ajandar taron koli kan tattalin arziki a farkon shekara. Ministan harkokin waje F-W Steinmeier ya ce zai tattauna da Rasha da zumar cimma sabuwar yarjejeniya game da samar da makamashi a Turai.

“Abin da muke bukata a Turai shi ne a samu wanzuwar demukiradiya da mulki na doka a Rasha don su dace da na Turai baki daya. Saboda haka na ke gani ya na da muhimmanci mu fadada yarjejeniyar hadin kai tsakanin mu da Rasha kana mu samar da wata sabuwar turba ta dangantaku, musamman wadanda suka shafi makamashi.”

A game da manufofin kudi, tattalin arziki, muhalli da kuma shari´a, dukkan ma´aikatun da wannan batu ya shafa sun yi tanade tanade da suka wajaba don samar da wani sabon tsarin shugabancin EU da zarar kasashen Portugal da Slovenia sun kammala wa´adin shugabancin su na kungiyar.

Bayan cikar wannan wa´adi a karshen watan yuni, watakila sai a shekara ta 2020 Jamus zata sake karbar shugabancin EU, idan za´a ci-gaba da bin tsarin karba-karba na shugabancin kungiyar.