1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubale gabanin zaben Zambiya

Usman Shehu Usman/GATAugust 10, 2016

An raunata mutane da dama a rikicin da ya barke kwanaki gabanin zaben shugaban kasar inda rikicin ke ta karuwa tsakanin magoya bayan manyan jam'iyyun siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/1JfGT
Sambia Lusaka Protest Opposition UPND
Hoto: Getty Images/AFP/D. Salim

Barkewar tashin hankalin dai ta sa hankula na kara tashi, a kasar da ake kwatantawa mai zaman lafiya. Duk da cewar a gobe Alhamis ake gudanar da zaben shugaban kasar, amma kawo yanzu ba alamar lafawar tashin hankalin, tsakanin magoya bayan manyan 'yan takara da ke kalubalantar juna. Hasali ma tarzuma sai kara bazuwa take yi.

Tun daga ranar Litinin dinnan ne dai tarzumar ta faro, bayan tsare wata motar safa, inda aka yi ta jifan 'yan siyasa da ke kan hanyar yakin neman zabe, abin da ya jawo raunata mutane da dama. An kuma ba da rahoton samun barkewar tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar. Ko da yake mutane tara ke takarar shugabancin kasar, amma dai rikicin ya fi muni tsakanin magoya bayan shugaba mai ci Edgar Lungu da magoya bayan Hakainde Hichilema, dan takaran babbar jam'iyar adawa. Shugaba Lungu ya lashe zaben shugaban kasa a zaben da ya gudanan bara, yayin da shi kuwa Hichilema ya kasance sau hudu yana takara ba nasara. Neo Simutanyi, wani mai sharhi kan siyasar Zambiya ya fada wa DW cewa.

"Yanayin siyasar ya dau zafi, mutane na cike da tsoron barkewar babban tashin hankali. Kuma ba alamar kawo karshen tashin hankali. Kwanaki biyu gabanin zaben, ba abin da ake gani illa kara munin tarzuma tsakanin magoya bayan jam'iyyun".

Hukumar zabe da 'yan takaran shugaban kasan duk sun yi Allah wadai da tarzumar da ta barke. Masana sun bayyana cewa, tarzuma da ake ganin a gangamin yakin neman zaben bana, ta kawar da sunan Zambiya a matsayin kasar da aka sani da zaman lafiya. To ko mi nene masanan ke ganin ya kawo tarzuma a zaben na bana sabanin yadda aka sani a baya?.

"Ina ganin gwamnati na son yin amfani da hargitsi don hana wa mutane zaben mutumin da suke so cikin kwanciyar hankali, kuma akwai batun zargin da ake yi wa hukumar zaben Zambiya, ko da sunayen masu kada kuri'a akwai rigima ciki. Har yanzu akwai sunaye sama da dubu 142 na masu kada kuri'a, wadanda duk sunayen suka zo daya. Wannan ya kawo rudani, kuma da wuya a shiga wannan zaben da tunanin zai gudana cikin lumana da adalci"

Ayar tambaya a nan ita ce, shin minene babban abin da zai fi daukar hankalin masu zabe a kasar Zambiya a wannan zabe? domin kuwa watanni sha tara kacal gwamnati mai mulki ta yi bayan zabenta a bara. Masanin siyasar kasar Zambiya Neo Simutanyi ya yi karin haske.

"Ina ganin batun tattalin arziki shi ne babban abin da ya fi damun jama'a. Ayar tambaya a nan ita ce, shin ko jam'iyya mai mulki za ta iya farfado da tattalin arzikin kasar, bisa la'akari da abin da ta yi shekaru biyar da take mulki? Domin an taba kawar da jam'iyya mai mulki a zabe, duk da cewa wancan lokacin komai na tafiya dai-dai. A gaskiyar lamarin yanzu tattalin arziki ya lalace fiye da yadda jam'iyyar ta tarda shi kan mulki. Ko da yake 'yan Zambiya basa la'akari da tattalin arziki in sun zo zabe"

Masana dai na cewa Shugaba Lungu ya yi kuskure wajen dauko mataimakiyar shugaban kasa daga bangaren da ba shi da magoya baya, domin a cewarsu, yin watsi da jihohin da ke matukar goyon bayan jam'iyarsa, hakan zai sa ko dai su kaurace wa kada kuri'a, ko kuma su jefa wa jam'iyyar da ke adawa da gwamnati. Yayin da shi kuwa madugun 'yan adawa Hichilema ke kokarin hawa kan mulki, bayan yunkurin hakan har sau hudu ba tare da samun nasara ba a baya.

Sambia Lusaka Wahlen Anhänger von Präsident Lungu
Hoto: Getty Images/AFP/G. Guercia
Sambia Nkole Mushula in Lusaka
Hoto: DW/C. Mwakideu