Kallo ya karkata filin jirgin saman Kaduna | Siyasa | DW | 08.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kallo ya karkata filin jirgin saman Kaduna

Za a dauki tsawon makonni shida ana aikin gyaran filin jirgin sama na Abuja, abin da ya sanya ake ganin ko na Kaduna zai iya aikin da yake yi.

A cewar jami'ai dai kamfani daya tilo da zai dauki aikin wato Julius Berger ya shirya tsaf  kuma ya kawo kayan aiki da nufin aikin da ake sa ran farawa jim kadan da kulle filin jirgin saman Abuja a tsakar dare na Laraba.To sai dai kuma rufe filin mai tasiri na nufin abubuwa daban-daban ga sassa daban na masu ci ta moriyarsa a yanzu. Ga fasinjojin da ke amfani da tashar  domin  sufuri ciki da ma wajen kasar dai daga dukkan alamu runguma ta kaddara na zaman karatu na da dama a tunanin Mohammed Murtala wani fasinjan da ke shirin zuwa birnin Legas a tashar.

A cikin neman gyara ko kuma kokari na kauce wa asara dai, a tunanin Dr. Ibrahim Yakubu Lame da ke zaman wani fasinjan daga Bauchi, ai ba ma mafita ga kokari na gyaran a cikin filin da ke kama da tarkon mutuwa yanzu. To sai dai in har sun karba ko ba dadi, ga su kansu masu sana'ar ta jiragen cikin gida dai na neman jajircewar duk da adawa ta waje. 

Har ya zuwa yanzu gwamnatin kasar na lallashi manya na kamfunan jiragen na waje da su koma ya zuwa ga Kaduna na tsawon makonnin guda shida,  amma na cikin gidan sun shirya domin dorawa a karatun na Abuja a fadar Monday Patrick da ke aiki da kamfanin Med View da ke  jigilar cikin gida.

To sai dai kuma ya zuwa yanzu dai mafi ji a jiki na zaman na kanana na masu kasuwa a cikin filin da tuni wasunsu ke korafin tai zafi kamar yadda  Sabiú Bello Hanafari wani mai sana'a ta salula da kati na waya ke fadi.

Akwai dai fatan gyaran zai kai karshen barazana da filin ya dade ya na fuskanta sakamakon lalacewa ta daben da ya kalli lalalcewar jirage da yawa can baya.

 

Sauti da bidiyo akan labarin