1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kai ɗauki a Pakistan

August 28, 2010

Pakisatan na fiskantar wata sabuwar masifar ambaliyar ruwa, don haka ake neman ƙarin agaji ga waɗanda lamarin ya shafa

https://p.dw.com/p/OyKN
Mata da yara ke neman abinci a PakistaniHoto: AP

Ƙungiyar tsaro ta NATO tace za ta tura ƙarin jiragen soji masu dakon kaya izuwa Pakistan domin kaiwa mutane ɗauki. A jiya ne dai wani jirgin dakon kaya yabar ƙasar Jamus, ɗauke da kayan agaji mai yawan gaske, wanda ya haɗa da injunan janareto da kayan samarda tsabtataccen ruwa, duk acikin agajin da gwamnatin Jamus ta yi alƙawarin bayarwa. A yau asabar ne wani jirgin dakon kayan zai bar ƙasar ta Jamus, ɗauke da wasu ijunan janareton samar da wuta, da jiragen kwale-kwale, da abinci da tufafi, wanda ƙungiyoyi masu zaman kansu ne suka bada tasu gudumarwar.

Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNICEF tace agajin da ƙasar Pakistan ke buƙata ya zarce yadda aka zata da fari nesa ba kusa ba. Hukumar tace ana buƙatar aƙƙalla euro miliyan fiyeda ɗari, da fari dai UNICEF ta buƙaci euro miliyan 36, amma yanzu tace lamarin ya zarce haka. Izuwa yanzu dai euro miliyan 27 kacal aka samu, kuma majalisar tace wannan babu inda zai kai, idan aka yi la'akari da yadda matsalar ke ƙaruwa. A halinda ake ciki dai an samu rohotonni wata ambaliyar sabuwa a ƙasar ta Pakistan, abinda ya tilastawa dubban daruruwan mutane barin gidajensu, don tsira. MDD tace kimanin mutane miliyan ɗaya suka bar gidajensu kama daga tsakiyar mako ,abinda kuma ya sa aka yi ƙiyasin cewa aƙalla kimanin mutane miliyan shida suna watangaririn neman wurin fakewa a faɗin ƙasar ta Pakistan.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abdullahi Tanko Bala