1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafar sada zumunta "Threads" ta fara aiki

Mouhamadou Awal Balarabe
July 6, 2023

Kamfanin Meta wanda a baya aka fi sani da Facebook ya kaddamar da sabuwar kafar sada zumunta na zamani mai suna Threads, wanda ke kamanceceniyar da Twitter wajen wallafa sako, kuma ya fitar da shi a iPhones da Android.

https://p.dw.com/p/4TTfV
Yadda ake samun Threads da ke zama sabuwar kafar sada zumuntaHoto: Mateusz Slodkowski/ZUMA/picture alliance

Kamfanin Meta ya jinkirta kaddamar da kafar Threads a nahiyar Turai saboda rashin samun izini daga hukumomin Brussels na Kungiyar Tarayyar Turai. Sabuwar kafar sada zumuntar wani bangare ne na Instagram da ke zama wani reshe na kanfanin Meta, kuma yana iya amfanar da mutane sama da biliyan biyu, kuma ba a tanadi amfani da tallace-tallace a wannan kafar ba ya zuwa yanzu.

sai dai sa'o'i hudu bayan kaddamar da Threads, Shugaban kanfanin Meta Mark Zuckerberg ya bayyana cewar fiye da mutane miliyan biyar sun yi rejista. Dama kanfanin Meta na fatan zama sabon dandamalin aikewa da sakon da aka fi so a duniya, lamarin da ka iya dakushe Twitter.