Kafa sabuwar gwamnatin haɗin kan Palasdinawa | Labarai | DW | 15.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kafa sabuwar gwamnatin haɗin kan Palasdinawa

P/M Palasɗinawa Ismaila Haniya na Hamas da shugaba Mahmoud Abbas na Fatah sun sanar da cimma yarjejeniya ta kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa. Shugabanin biyu sun cimma daidaito a kan wanda zaá naɗa a mukamin ministan kula da alámuran cikin gida matsayin da ya hana ruwa gudu a yunkurin kafa sabuwar gwamnatin. P/M Ismaila Haniya yace zaá sanar da sunayen Ministocin a kuma rantsar da su a yau Lahamis a Gaza. A ranar Asabar mai zuwa majalisar dokoki zata kaɗa ƙuriár amincewa da gwamnatin haɗin kan ƙasar.