1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafa sabuwar gwamnatin haɗin kan Palasdinawa

March 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuPc

P/M Palasɗinawa Ismaila Haniya na Hamas da shugaba Mahmoud Abbas na Fatah sun sanar da cimma yarjejeniya ta kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa. Shugabanin biyu sun cimma daidaito a kan wanda zaá naɗa a mukamin ministan kula da alámuran cikin gida matsayin da ya hana ruwa gudu a yunkurin kafa sabuwar gwamnatin. P/M Ismaila Haniya yace zaá sanar da sunayen Ministocin a kuma rantsar da su a yau Lahamis a Gaza. A ranar Asabar mai zuwa majalisar dokoki zata kaɗa ƙuriár amincewa da gwamnatin haɗin kan ƙasar.