Kafa gwamnati a kudancin Sudan | Labarai | DW | 20.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kafa gwamnati a kudancin Sudan

Shugaban kudancin Sudan Salva Kiir yace yankinsa ba zai jira har sai gwamnatin birnin Kahrtoum ta amince da kundin tsarin mulkinsa kafin ya kafa wata gwamnati ba. Kiir wanda har wayau shine shugaban tsohuwar kungiyar ´yan tawayen kudancin Sudan ta SPLM ya ce wannan mataki yana da muhimmanci wajen sake gina wannan yanki da yaki ya daidaita. To sai dai bai ambaci sunayen mutanen da zai a ba wa mukaman ma´aikatu sama da 20 na gwamnatin yankin ba. To amma ya ce za´a yi haka kafin ma´aikatar shari´a ta gwamnatin Sudan ta amince da kundin tsarin mulkin wanda a halin yanzu ake tattaunawa a kai. Ya ce matakin na daga cikin ka´idojin yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da suka amince da ita a cikin watan janeru da nufin kawo karshen yakin basasan da aka shafe shekaru 21 ana yi.