1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fahimtar juna tsakanin Conte da Macron

Mohammad Nasiru Awal LMJ
June 15, 2018

Sabon Firaministan Italiya Giuseppe Conte da Shugaban Faransa Emmanuel Macron sun goyi da bayan kirkiro da cibiyoyin karbar takardun masu neman mafakar siyasa a kasashensu na asali.

https://p.dw.com/p/2zeNE
Frankreich - Marcron empfängt italienischen Premierminister Conte
Hoto: picture-alliance/abaca/B. Eliot

A takaddamar da ake yi game da matakan karbar 'yan gudun hijira a nahiyar Turai, sabon Firaministan Italiya Giuseppe Conte da Shugaban Faransa Emmanuel Macron sun goyi da bayan kirkiro da cibiyoyin karbar takardun masu neman mafakar siyasa a kasashensu na asali.

Macron ya ce yana goyon bayan shawarar bude rassa na hukumomin da ke duba bukatun masu neman mafakar siyasa domin warware wannan batu tun a kasashen arewacin Afirka da ke a gabar tekun Bahar Rum. Shugaban na Faransa ya kuma yi kira da a kara tallafa wa Italiya a kan matsalar 'yan gudun hijira.

Ya ce: "Faransa kamar Italiya tana fama da matsalar bakin haure ya zama kuma dole mu hada kai domin samun maslaha. Za mu kuma yi aiki da sauran kasashen EU don yin wani abu kwakkwara da bai take hakkin dan Adam ba don samun mafita."

Ya kuma yi kira da a yi wa manufofin kungiyar EU kan gudun hijira kwaskwarima.

Ya kuma yi kira ga Firaministan na Italiya da ya yi aiki tare da Faransa da Jamus da Spaniya wajen warware batutuwan na 'yan gudun hijira maimakon ya goyi bayan wata kungiyar masu kyamar baki da ke kunno kai a cikin kungiyar EU.