Kace nace a game da kisan kiyashi kan bani yahudu | Labarai | DW | 23.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kace nace a game da kisan kiyashi kan bani yahudu

Kasar Amurka ta shirya gabatar da kuduri a gaban babban zauren Mdd,da zai nemi yin Allah wadai da wadanda suke karyata afkuwar kisan kiyashi akan bani Yahudu.

Wannan kuduri, a cewar rahotanni bai fito fili ya ambaci sunan wata kasa ba, to sai dai kudurin yazo ne wata daya bayan Iran ta shirya wani taro na karyata faruwar kisan kiyashin akan bani yahudun.

A lokacin tattaunawar, da yawa daga cikin mahalarta taron sun karyata faruwar wannan abu akan bani yahudun , wasu kuma na da ra´ayin cewa ya faru amma anyi karin gishiri akan faruwar tasa.

A cewar kakakin Amurka a Mdd, tuni aka rarraba kwafin

Kudurin ga wakilan majalisar, don ya dace da rana ta musanman , wato 27 ga watan nan, don tunawa da kisan kiyashin da akayiwa bani yahudun.