Kabila zai ci gaba da mulki, idan aka jinkirta zabe a Kwango | Labarai | DW | 11.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kabila zai ci gaba da mulki, idan aka jinkirta zabe a Kwango

Kotun tsarin mulkin kasarce ta zartar da cewar Joseph Kabila zai zauna kan karagar mulki har bayan wa'adin mulkinsa, idan har gwamnatinsa ta gaza gudanar da zabe a watan Nuwamba.

Hukuncin kotun dai wani babban koma baya ne ga 'yan adawa, wadanda suka jaddada bukatar kafa gwamnatin wucin gadi a karshenh wa'adin mulkin kabila, idan har an samu jinkiri wajen gudanar da zaben kasa.Tun a shekarata 2001 ne dai Kabila ya dare karagar mulki, bayan kisan gilla da aka yi wa mahaifinsa wanda yake shugaba a wancan lokaci. Bayan wa'adin mulki na shekaru biyar wanda zai kare a Nuwamba, kundin tsarin mulkin Kwagon ya tanadi saukarsa daga mulki.

A birni na biyu mafi girma na Lubumbashi, 'yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye domin wargaza gangamin dubban magoya bayan Moise Katumbi, babban dan takarar kujerar shugaban kasar daga bangaren adawa da ke fuskantar shari'a, sakamakon zarginsa da gwamnatin kasar ke yi da dauko sojojin haya daga ketare domin fada a kasar.Gwamnatin Janhuriyar demokradiyyar Kwagon dai ta ce akwai yiwuwar jinkirta zaben, saboda karancin kudi da kayayyakin gudanar da zaben.