Köhler ya buɗe babban taro kan nahiyar Afirka a nan Jamus | Labarai | DW | 03.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Köhler ya buɗe babban taro kan nahiyar Afirka a nan Jamus

A hukumance shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler ya bude babban taro kan nahiyar Afirka karo na uku. Köhler wanda ya kirkiro wannan taron tsakanin Jamus da kasashen Afirka, ya fadawa mahalarta taron kimanin 44 cewa har yanzu babu cikakkiyar masaniya tsakanin kasashen duniya duk da ingantuwar dangantaka tsakanin kasa da kasa. Daga cikin mahalarta taron akwai shugabannin kasashen Mozambik, Botswana, Nigeria da Benin sai kuma mawallafin nan dake zama a Afirka da Sweden wato Henning Mankell. A danganer da kalubalen da ake fuskanta na hadakar manufofin tattalin arzikin duniya, taken taron shi ne kalubaloli na sauyi, wane irin martani Afirka da Jamus zasu mayar?