Köhler a tarayyar Nijeriya | Siyasa | DW | 07.11.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Köhler a tarayyar Nijeriya

Ziyarar shugaban Jamus Horst Köhler a tarayyar Nijeriya.

default

Shugaban Jamus Köhler lokacin ziyararsa a Rwanda

A yau Juma´a shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler ke fara wata ziyarar kwanaki shida a tarayyar Nijeriya, inda zai halarci taron ƙarfafa dangantaka da nahiyar Afirka wanda shugaban na Jamus ya ƙirƙiro. Zai kuma tattauna da shugabannin Nijeriya akan batutuwa da dama ciki har da samar da sahihiyar demoƙuraɗiyya da kuma shugabanci nagari a nahiyar Afirka.

Jim kaɗan kafin shugaban na tarayyar Jamus Horst Köhler ya tashi zuwa Nijeriya a wannan ziyarar dake zaman irinta ta huɗu zuwa nahiyar Afirka, domin halartar taro karo na huɗu kan ƙarfafa dangantaka da wannan nahiya, ƙungiyar kare haƙin Bil Adama ta Human Rights Watch (HRW) ta aike masa da wata buɗaɗɗiyar wasika wadda a ciki ta nemi shugaban na tarayyar Jamus da ya taɓo batutuwa da dama ciki har da batun kare haƙin bil Adama da matsalar cin hanci da rashawa a tattaunar da zai yi da hukumomin Nijeriya. A lokacin da take tsokaci game da kiran da ƙungiyar ta HRW ta yiwa shugaba Köhler Marianne Heuwagen ta yi nuni da cewa hukumomi a tarayyar Nijeriya suna fatali da haƙin ɗan Adam.

Ta ce: "Har yanzu ana kawad da ido daga masu aikata laifin keta haƙin ɗan Adam. Alal misali a wurare da dama ´yan sandan Nijeriya na da hannu a fatattakar da ake yiwa wasu ɗaiɗaikun ƙungiyoyi. Kana kuma ana cusa ƙiyayya tsakanin al´ummomin wannan ƙasa. Duk da haka ba a bin diddigin masu aikata wannan laifi sannan ba a bari shari´a ta yi aikinta yadda ya kamata."

Ƙungiyar HRW ta kuma yi zargin cewa cin hanci da rashawa da yayiwa tarayyar ta Nijeriya katutu na kawo ciƙas wajen samarwa al´umar ƙasar muhimman abubuwa na more rayuwa. Marianne Heuwagen ta ce duk da dubban miliyoyyin daloli da Nijeriya mai arzikin man fetir ke samu daga cinikin wannan haja ta ta, talakawan ƙasar ba sa gani a ƙasa.

Ta ce: "Babu isassun kayan karatu ga ƙananan yara. Ana fama da ƙarancin muhimman abubuwan more rayuwa sannan al´umar ƙasar na cikin hali na talauci saboda rub da ciki da wasu shugabannin siyasa ƙalilan da muƙarabbansu ´yan kasuwa ke yi da arzikin ƙasa maimakon su ɗauki ƙwararan matakan yaƙi da talauci."

HRW na mai ra´ayin cewa Jamus za ta iya taimakawa Nijeriya wajen yaƙi da cin hanci da rashawa fiye da a lokutan baya. A wata tattaunawar da manyan jami´an hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin Nijeriya ta´annati suka yi da ƙungiyar a bara sun nuna damuwarsu ga rashin samun cikakken haɗin kai tsakanin hukumar da gwamnatin Jamus.

A dangane da wannan mummunan ci-gaban HRW ta yi roƙo ga shugaba Köhler da ya nema da shugaba ´Yar Adua da gwamnatinsa da su yiwa jama´a bayani game da binciken da ake yiwa wasu shugabannin siyasa da ´yan kasuwa dake azurta kansu da dukiyar ƙasa da kuma binciken da ake yiwa wasu kamfanonin Jamus na cin hanci da rashawa a Nijeriya.

Baya ga birnin Abuja shugaban na Jamus zai kuma kai ziyara a biranen Lagos da kuma Kano.

Sauti da bidiyo akan labarin