1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Köhler a Afurka

April 11, 2006

A yau shugaban kasar Jamus Horst Köhler ke kammala ziyararsa ga nahiyar Afurka

https://p.dw.com/p/Bu0h
Köhler a Botswana
Köhler a BotswanaHoto: AP

Akwai banbance-banbancen ci gaba mai tsananin gaske a tsakanin ƙasashe ukun da Horst Köhler ya kai musu ziyara a cikin kwanaki goman da suka wuce. Shugaban na Jamus ya ce ba za a iya kwatanta ƙasashen Afurka tamkar dukkansu jirgi ɗaya ne ke ɗauke da su ba. Kowace ƙasa ta nahiyar na da alƙiblar da ta fuskanta. Bruno Wenn, darektan bangaren taimakon kasashen Afurka dake kudu da hamadar sahara a cibiyar rancen sake ginawa ta Jamus yayi bayani game da waɗannan banbance-banbance yana mai cewar:

“Ƙasar Botswana ta zarce matsayin da yawa daga ƙasashe masu tasowa, inda a yanzu haka al’umar ƙasar ke samun abin da ya kai dalar Amurka dubu hudu idan an kwatanta da jumullar abin da take samarwa a shekara, a yayinda ƙasashen Muzambik da Madagaskar ko kusa da hakan ba su yi ba duk kuwa da kyakkyawar bunƙasar tattalin arzikin da suke samu bisa manufa.”

Shugaban ƙasar Horst Köhler ya bayyana gamsuwarsa da ziyarar da ya kai ga ƙasashen guda uku, wadanda shi kansa ne ya zaɓesu a balaguronsa na biyu ga nahiyar Afurka a matsayinsa na shugaban ƙasar Jamus. Köhler ya ƙara da cewar:

“Dadai da yadda nayi tsammani tun farko waɗannan ƙasashe guda uku suna kan hanya madaidaiciya a ƙoƙarinsu na raya makomarsu ko da yake dukkansu na sane da cewar har yau suna da sauran tafiya a gaba.”

Bisa ga ra’ayin shugaban na Jamus, babban alhakin da ya rataya a wuyan Turawa shi ne su tashi tsaye wajen mara wa ƙasashen Afurka baya ta la’akari da tarihi bai ɗaya dake tsakaninsu. Muddin ƙasashen Afurka ba su samu ci gaba daidai yadda ya kamata a cikin ɗan lokaci nan gaba ba to kuwa ita kanta nahiyar Turai zata sha fama da raɗaɗin lamarin. Wani abin da aka lura da shi a ziyarar ta Köhler a ƙasashen Muzambik da Madagaskar kuma shi ne rashin hadin kan manufofin raya ƙasa tsakanin ƙasashen dake ba da taimako. Wannan rashin daidaiton na taimakawa wajen bunƙasa matsalar cin hanci tare da haifar da nawa ga ita kanta ƙasar dake samun taimakon. Köhler yayi kakkausan suka game da daruruwan shirye-shiryen raya masana’antu da kuma da neman cusa wa ƙasashen Afurka wasu ra’ayoyin da ko kaɗan ba su dace da yanayinsu ba. Ya ce abu mafi alheri shi ne a ba da goyan baya ga ra’ayin su kansu ƙasashen na Afurka a game da hanyar da suke ganin ita ce zata taimaka musu wajen raya makomarsu.