Juyin mulkin farko a nahiyar Afrika
October 7, 2010Talla
Ƙasar farko da ta fara shirya juyin mulki a Afrika itace ƙasar Masar a shekara 1952 inda Mohamed Naguib ya kifar da mulkin Sarki Farouk na ɗaya.
Sai kuma a shekara 1958 a ƙasar Sudan mai maƙwabtaka da Masar inda Ibrahim Abdoud ya hamɓarar da shugaba Abdoullah Khalil.
A yankin yammacin Afrika kuwa ƙasar Togo ce ta fara ɗanɗana uƙubar juyin mulki a shekara 1963 shekaru uku bayan samun ´yancin kai, inda Emmanuel Bodjollé ya kifar da zaɓɓaɓen shugaba na farko Sylvanius Olympio.
Daga ƙasar Togo ne al´adar juyin mulkin ta bazu a sauran ƙasashen Afrika maƙwafta, kamar su Mali, Burkina Faso, Jamhuriya Nijar, Tarayya Najeriya da dai sauran su.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Ahmed Tijani Lawal