Juyin mulki ya tabbata a Fiji | Labarai | DW | 06.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Juyin mulki ya tabbata a Fiji

Jogoran kifar da gwamnati a tsibirin Fiji ,Commander Frank Bainimarama ,ya bayyana cewa rundunar soji zasu dauki dukkan matakan wani tashin hankali daka auku sakamakon ,wannan juyin mulki.Wannan furuci nasa dai sunzo ne sakamakon,kiran da hambarren premiern Fuji Mr Qarase yayi ,nacewa a gudanar da bore na lumana a kann wannan juysin mulki.Dakarun Soji nedai suka rakaMr Qarase daga babban birnin kasar dake Suva.Yini guda da hambarar da mulkin wannan kasa dake kudancin Facifik,Commander Bainimarama ya sanar da dokar ta baci ,bayan rusa majalisar dokokin kasar,tare da nada ministan rikon kwarya.