Juyin mulki nawa aka yi Afirka daga samun yancin kan ƙasashen zuwa yanzu ? | Amsoshin takardunku | DW | 01.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Juyin mulki nawa aka yi Afirka daga samun yancin kan ƙasashen zuwa yanzu ?

Daga samun yancin kan Afirka zuwa yanzu, sojoji sun yi juyin mulki kussan 70 a ƙasashe daban-daban.

default

Moussa Dadis Camara, ɗaya daga sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea

Juyin mulki nawa aka yi  Afrika daga samun ´yancin kan ƙasashen nahiyar zuwa yanzu ?

Ɗaya na bin ɗaya sojoji sun shirya juyin mulki har sau 67 a Afrika.Sannan sunyi yunƙurin juyin mulki wanda ba shi misaltuwa.

Juyin mulkin farko dai an shirya shi a ƙasar Masar a shekara 1952, inda Mohamed Naguib ya hamɓɓarrar da Sarki Farouk na ɗaya.

Sai a shekara 1958  a ƙasar Sudan inda Ibrahim Abdoud ya kifar da mulkin Abdoulah Khalil.

A shekara ta 1963 ƙasashe biyu na Afrika suka fuskanci juyin mulki, ta farko itace Kongo inda David Moussaka tare da haɗin gwiwar Felix Mouzabakani suka kifar da Fulbert Youlou daga gadon mulki.

Sai kuma ƙasar Togo inda Emmanuel Bodjole ya hamɓɓare Sylvanious Olympio shugaban ƙasar na farko bayan samun yancin kai.

A shekara 1965 nan ma an samu juyin mulki biyu.A Aljeriya Houari Boiumediéne ya ƙwace mulki daga Ahmed Ben Bella, sai kuma a Zaire inda Mubutu Sese Seko ya ture Joseph Kasa-Vubu.

Shekarar da aka fi yawan fuskantar juyin mulki itace 1966.A wannan shekara ƙasashe biyar aka kifar da muli a cuikinsu:

Kinga dai akwai Haute Volta wato Bourkina Faso ta yanzu inda Sangoule Lamizana ya kifar da Maurice yameogo, sai BUrundi inda Michel Micombero ya ture Ntare V.A jamhuriya Afrika ta Tsakiya Jean Bedel Bokassa ya juye David Dacko.

A Taraya Nigeria, Johson Aguiyi Irons,i ya hamɓarar da Nnandi Azikwe.Sai kuma Uganda inda Milton Obote yayi wa Edward Mutesa juyin mulki.

A shekara 1968 sojojin ƙasar Mali bisa jagoranci Musa Traore suka kifar da Modibo Keita.

A shekara 1969 Afrika ta fuskanci juyin mulki guda biyu a ƙasar Libiya inda Mouammar Ƙhaddafi ya sauke Idris na daya, saikuma Sudan inda Gaffar Nimeri ya juye Ismail Alzahari.

A shekara 1971 Uganda ta fuskanci juyin mulkinta na biyu, inda Idi Amin Dada ya sauke Milton Obote.

A shekara 1973 a ƙasar Ruwanda Juvenal Habyarimana ya kifar da shugaba Gregoire Kayibanda.

Shekara 1974 anyi juyin mulki ukku, biyu a ƙasar Ethiopiya ɗaya a Niger.

A Ethiopiya Aman Andom ne ya kifar da Haile Selassier na daya kafin shima Mengistu hiale Haile maryam ya ramawa kura aniyarta ta hanyar sauke ba tare da bata lokaci ba.

A Jamhuriya Niger Litanan kalan Seiyni Kountche ya kifar da shugaba Diori Hamani.

A shekara mai zuwa 1975 sojoji sun yi juyin mulki huɗu a Afrika:

A Jamhuriya musulunci ta Comoros Said Mohamed Jaffar ya ture Ahmed Abdellah.

A Nigeria Yakubu Gawan ya  kifar da Johnson Aguiyi-Ironsi, sai kuma Tchadi inda Noel Milarew Odingar ya hamɓɓara da Franßois Tombalbey.

Shekara ta gaba wato 1976 nan juyin mulki biyu aka yi anyi a BUrundi inda Jean-Baptiste Bagaza ya sauke Michel Micombero.Sannan a Jamhuriya Musulunci ta Comoros aka yi na biyu inda Ali Soilih ya kifar da Said Mohamed Jaffar ba tare da yi  shekara ɗaya bisa mulki ba.

Sai a shekarar 1977 a Congo Joachim Yhombi-Opango yayi wa Marien Ngouabi.

Sai kuma Ethiopiya inda Mangistu Haile Maryam ya jagoranci juyin mulki na biyu ta hanyar kiffar da shugaba Tafari Benti.

A shekara 1978 Jamhuriya Musulunci ta Comoras ta ƙara faɗawa cikin juyin mulki inda Said Atthoumani ya sauke Ali Soilih.

Sai kuma ƙasar Mauritaniya inda Mustafa Ould Salek ya kifar da gwamnati Moktar Ould Dadah.

A shekara 1979 juyin mulki huɗu aka shirya a Afrika a Equatoriale GUinea Teodore Obiang Nguema Mbasogo ya hamɓɓare Fransisco Macias Nguema.

Sai a Jamhuriya Afrika ta tsakiya David Dacko ya ɗauki fansa ga Jean Bedel Bokassa.A ƙasar Chadi Goukouni Oueddei ya juye mulkin Felix Maloum.Sai  a Uganda Yasufu Lule ya sauke Idi Amin Dadah.

A shekara 1980 nan ma juyin mulki ukku aka shirya, a Burkina Faso Saye Zerbo ya ya kifar da Sangoulé Lamizana, sai a  Guinea Bissau Joao Bernardo Vierra ya kifar da mulkin Luis de Almeida Cabral, kamin a ƙasar Liberia samuel ya ƙwaci mulki da tsinin bindiga daga Wiliam Richard Tolbert.

To yanzu sai mu shiga shekara ta 1981 wadda Afrika ta samu juyin mulki ɗaya tilo a Jamhuriya Afrika ta Tsakiya, inda Andre Kolingba ya ture David Dacko.

A shekara 1982 Tchad da Bourkina Faso, sun ƙara faɗawa cikin halin juyin mulki.

A Bourkina ko kuma Haute Volta ,Jean Baptiste Ouedrago,ya juye saye Zerbo sai kuma a Chadi Hisséne Habre ya kori Goukkouni Oueddei.

A shekara ta gaba wato 1983 kuma dai a Haute Volta an shirya wani juyin mulkin, wanda a cikin sa kaftan Thomas Sankara mai ra´ayin juyin juya hali, ya kifar da  Jean Baptiste Ouedrago kuma ya cenza sunan ƙasar daga Haute Volta zuwa Bourkina Faso.

A wannan shekara ce a Nigeria Janar Muhamad Buhari ya kori Shehu Shagari daga kujera mulki.

A shekara 1984 juyin mulki biyu a Afrika, wanda suka haɗa da Guinea Conacry inda Lansana Conte ya kori Louis Lansana Beavogui.Sannan a Mauritaniya Ma´aouiya Ould Tayya ya kifar da shugaba Mohamed Khouna Ould Haidallah.

A shekara 1985 a ƙasar Uganda Basilio Olara Okello ya kori Milton Obote, sa a Sudan Swar Al-Dahab ya kifar da mulkin Gaafar Nimeiry.

A shekara ta gaba kuma Sudan ta ƙara fama da wani juyin mulkin, inda Ahmed al-Mirghani ya hamɓarra da Swar al-Dahab.

A shekara 1987 a ƙasashe uku sojoji suka gudanar da juyin mulki.Sun sake yi a Bourkina faso inda Blaise baban dogari mai gadin  shugaba Thomas Sankara ya bindige mai gidan nasa, ya haye kujerarsa.

Sai Burundi inda Pierre Buyoya ya kifar da Jean Baptiste Bagaza, sannan a Tunisiya Zine el Abidine Ben Ali, wanda har yanzu ke kan karagar mulki ya kifar da shugaba Habib Bourgiba.

A shekara 1989 Sudan ta kara komawa cikin juyin ulki inda shugaba mai ci yanzu Omar Al-Beshir ya kori Ahmad al-Mirghani daga kujera mulki..

A shekara 1990 ƙasar Liberia kaɗi ta yi juyin tare inda Princ Johson ya gama da samuel Do, wanda suka ganewa idonsu al´amarin ta hanyar TV ƙila zasu iya tunawa yadda akayi gunduwa-gunduwa da gawar Samuel Do.

Pina mu ƙara shaƙatawa kamin mu cigaba.

To sai kuma shekara 1991 wato lokacin kaɗawar sabuwar guguwar demokradiya a Afrika, inda a ƙasar Mali  Janar Amadou Toumani Toure mai mulki yanzu haka ya kifar da mulkin Moussa Traoré.

Shekara ta gaba hukumar koli ta tsaron ƙasa ta sauke Chadli Bendjedid daga mulki.

Daga nan Afrika ta sarara har tsdawan shekaru ukku ba tare da an fuskanci juyin mulki , sai kuma kwatsam! a Jamhuriya musulunci ta Comoros a shekara 1995 Ayoub Combo ya hamɓarrar da shugaba said Mohamed Johar.

A shekara 1996 a Burundi Pierre Buyoya ya kifar da gwamnatin shugaba Syvestre Ntibantuganiya, sannan a Jamhuriya Niger Ibrahim Mainasara Ba´are ya kifar da shugaba Mahaman Usman sakamakon wani rikicin siyasa da ya ki ƙamari tsakanin  gwamnati da ´yan adawa.

Shekara ta gaba1997 a ƙasar Zaire wato Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo ta yanzu, Laurent Desire Kabila yayi wa Mbutu Sese Seko juyin mulki.

Sai shekara 1999, inda aka kilga juyin mulki har huɗu a Afrika:

A Comoros Azali Asoumani ya kori Tadjidine Ben said Massounde.

A Cote d´Ivoire Robert Guie ya hamɓarar da mulkin Henri Konen Bedie.A Guinea Bissau Assumane Mane ya kifar da Joao Bernardo Vierra.Sai kuma Niger inda sojoji bisa jagorancin Dauda Mallam Wanke suka bindige har lahira shugaba Ba´are Ibrahim Mainasara.

A shekara 2003 Franßois Bouzize da ke kan karagar mulki har yanzu ya kifar da mulkin Ange Felix Patase.Sannan a Guinea Bissau Verrissiom Correira Seabra ya hamɓar da Kumba Yala.

A shekara 2005 a ƙasar Mauritaniya ne kawai akayi juyin mulki inda Ely Ould Mohamed Vall ya kifar da gwamnatin Ma´aouwiya Ould tayya.

har yanzu yanzu a Mauritaniya a shekara 2008 Mohamed Ould Abdel Aziz ya kori shugaba Sidi Mohamed Ould  Cheick Abdullahi.

A Guinee  a ƙarshen shekara ta 2008 bayan mutuwar Janar Lansana Konte,Moussa Dadis Kamara ya ɗare kujera mulki abinda ke matsayin wani sallo na juyin mulki.

A shekara 2009 a ƙasar Madagascar sojoji sun kori shugaban ƙasa Marc Ravalomanana, suka kuma ɗora farra hulla Andry Rajoelina.

Juyin mulki na baya bayan nan shine wanda ya faru a Jamhuriya Nijar, inda sojoji bisa jagorancin Salou Djibbo suka sauke shugaban ƙasa Tanja Mamadou, kuma suka ce zasu maido da demokraɗiya.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Zainab Mohamed Abubakar