1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Juyin Mulki A Nijer

Tijani LawalFebruary 19, 2010

Bayan kai ruwa ranar da aka sha famar yi a siyasar Nijer sojoji sun ƙwace ragamar mulki

https://p.dw.com/p/M5mx
Hamɓararren shugaba Mamadou Tanja na NijerHoto: AP

A wannan makon ma dai kamar a makon da ya gabata, jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni iri daban-daban akan al'amuran nahiyarmu ta Afirka. Za dai mu fara ne da rahoton jaridar Süddeutsche Zeitung, wadda ta leƙa Nijer domin duba abin dake faruwa a ƙasar ta yammacin Afirka. Jaridar ta ce:

"A ranar jiya alhamis sojojin sun karɓe ragamar mulki a ƙasar Nijer, bayan da suka kutsa fadar shugaban ƙasa Tanja suka kuma tasa ƙeyarsa lokacin wani zama na majalisar ministoci. Shi dai shugaban dake mulki tsawon shekaru goma da suka wuce sai da ya fuskanci matsin lamba sakamakon fafutukar da riƙa yi na yin ta zarce ko ta halin ƙaƙa."

Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung sai da ta tofa albarkacin bakinta akan juyin mulkin na Nijer inda take cewar:

"Tsofon soja Mamadou Tanja, wanda tun a shekara 1999 yake mulki a Nijer, sai ta ya tilasta canza daftarin tsarin mulkin ƙasar ala-dole a cikin watan disemban shekara ta 2008 domin samun kafar yin ta zarce akan karagar mulki. A sakamakon adawar da ya fuskanta akan wannan manufa Tanja ya ɗauki matakin rushe majalisar dokoki da kotun ƙoli ta ƙasar, lamarin da daga bisani ya zama masa alaƙaƙai a manufofi na cikin gida."

 A can ƙasar Kenya ma ana fama da kai ruwa-rana dangane da siyasar ƙasar a cewar jaridar Süddeutsche Zeitung. Jaridar ta ƙara da cewa:

"Shekaru biyu bayan kawo ƙarshen tashin-tashinar siyasa da zub da jini a halin yanzu haka matsalar cin hanci da gwagwarmayar kama madafun mulki shi ne ke barazana ga makomar gwamnatin ƙasar Kenya. Da yawa daga al'umar ƙasar na tattare da ƙyama da kuma tsaro game da yadda al'amuran siyasa ke tafiya, inda jami'an siyasa suka gaza wajen gabatar da nagartattun matakai na garambawul da tantance maguɗi da almundahana tsakaninsu."

A can ƙasar Cote d'Ivoire ma an shiga wani sabon hali mawuyaci a game da siyasar ƙasar bayan da shugaba Laurent Gbagbo ya rushe gwamnati, kuma 'yan adawa farar hula su ne suka fi shan raɗaɗin wannan gwagwarmaya na kama madafun mulki. Sai dai kuma kawo yanzu 'yan tawaye ba su ce uffan ba a cewar jaridar Die Tageszeitung, wadda ta ƙara da cewar:

"A dai halin da ake ciki yanzu ƙasar Cote d'Ivoire na fuskantar barazanar sake faɗawa cikin wani sabon yanayi na tashe-tashen hankula. An dai sha soke zaɓuɓɓuka na demoƙraɗiyya da akan shirya a shekarun baya-bayan nan kuma wa_adi na ƙarshe da aka soke shi ne na ranar 29 ga watan nuwamban da ya wuce. Tuni dai 'yan tawaye suka saka dakarunsu cikin shirin ko ta-kwana, kuma zaman lafiya ko rashinsa a ƙasar ta Cote d'Ivoire ya danganta ne da natakin da zasu ɗauka."

Rahotanni sun ce tun abin da ya kama daga ƙasar Mali a yammaci da Somaliya a gabacin Afirka an fara samun wasu ƙungiyoyi na 'yan sunƙuru dake kunno kai. A lokacin da take ba da wannan labarin jaridar Neues Deutschland cewa tayi:

"Tsakanin kusurwa uku na ƙasashen Mali, Alijeriya da Nijer ana daɗa samun wasu sansanoni na ƙyanƙyashe 'yan ta'adda kuma ma a yanzu ƙungiyar al-ƙa'ida ƙoƙari take yi na yaɗa angizonta a Nijeriya. A can Somaliya kuwa ƙungiyar ce ummal'aba'isin rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a ƙasar. A dai halin yanzu ƙungiyar sai yaɗa angizonta take yi a nahiyar Afirka a ƙoƙarinta na yaɗa abin da ta kira wai jihadi na gama gari a duk faɗin duniya."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Zainab Muhammed Abubakar