1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Juyin mulki a ƙasar Mauritaniya.

Yahouza, SadissouAugust 11, 2008

Ƙasar Mauritaniya ta shiga saban rikicin siyasa, bayan da sojoji suka hamɓara da shugaban ƙasa Ould Abdullahi.

https://p.dw.com/p/Euun
Juyin mulki a MauritaniyaHoto: picture-alliance/dpa


Masu sararo asalamu alaikum barka mu da warhaka, lale marhabin da sake saduwa daku a wani saban shiri, na duniya mai yayi, shirin da kan gabatar maku da bayyanai a game da harakokin siyasa a duniya, da kuma faɗi  tashin tsirarun ƙabilu.

A wannan karo, shirin zai je da mu ƙasar Mauritaniya, inda a farkon watan da muke ciki, sojoji suka hamɓara da shugaban ƙasa Sidi Ould Cheick Abdullahi, daga karagar mulki.

Za mu yi waiwaye adon tafiya,a game da harakokin siyasa a wannan ƙasa, da kuma illolin da juyin mulkin ya jawo.

Nine Yahouza Sadissou Madobi, ke farfin kasancewa tare da ku.


Ƙasar Mauritaiya na da yawan mutane miliyan ukku da ´yan ka, ta na iyaka da ƙasashen Mali, Senegal, Algeria, yankin kudancin Sahara, da kuma tekun Bahrum.

Ƙasar ta samu yancin kanta, daga turawan mulkin mallakar ƙasar France a  shekara ta 1960, bisa jagorancin shugaba Moktar Ould Daddah.

Ta fannin juyin mulki kuwa wannan sine karo na hudu da sojoji na hamɓara shugaban kasa.

Juyin mulkin farko ya wakana a shekara ta 1978 inda Klan Ould Seck ya hamɓara da shugaba Mokthar Ould Dadah.

Sai kuma  shekara ta 1984 Klan Mou´awiya Ould Taya, ya hamɓara da shugaban ƙasa Momahed Khouna Oul Haidallah, bayan shekaru huɗu ya na jagorancin Mauritaniya.

A watan Ogust na shekara ta 2005, Janar Ely Ould Mohamed Vall, ya jagorancin ayarin sojojin da suka ture shugaban ƙasa Ould Taya  ayayin da ya ke cikin bulaguro a ƙasar Saudi Arabiya.

Sojojin sun girka gwamnatin riƙwan ƙwarya wadda ta shirya zaɓen raba gardama wanda ya haifar da saban kudin.

kazalika, ta shirya zaɓen ´yan majalisun dokoki da na shugaban ƙasa.

A sakamakon wannan zaɓe Sidi Ould Cheick Abdullahi ya zama shugaban ƙasa.

Saidai ba aje ko ina ba, ƙasar Mauritaniya ta sake faɗawa cikin wani saban  rikicin siyasa wanda a sakamakon sa sojojin ƙasar, bisa jagorancin Jannar Mohamed Ould Abdel Aziz, shugaban rundunar sojojin fadar shugaban ƙasa ta kaddamar da juyin mulki a farkon watan da muke ciki.

.................................

Wanan juyin muli da ya wakana a ƙasar mauritaniya ya sha suka matuka daga sassa dabam dabam na duniya to saidai cemma masu kulla da harakokin siyasa  a kasar sunce sun san cemma  arina ta la´kari da baddaklalar da afgensiyasar ya shiga, Mustafa Ould Abdurahman dan Majalisar dokoki ne,a banagren jam´iyu amsu rike da ragamar mulki, yana kuma daga masu wannan ra´ayi:


" Tun watanni a ƙalla biyu da suka wuce, jam´iyun siyasa masu rinjaye  a Majalisar Dokoki, suka yi kira ga gwamnati ta cenza halayenta.

Misali, shugaban ƙasa ya maida  ƙasa baya, ta hanyar sake maido tsafin kuraye, wanda sojoji suka hamɓare a shekara ta 2005.

Bayan wannan ana fuskantar matsaloli masu yawa, matsala ta bayan bayan nan, itace yadda gwamnati ta haramtawa Majalisar Dokoki shirya taron gaggawa na mussamman, domin tattanawa akan wasu matsaloli masu mahimmanci da suka shafi tafiyar ƙasa.

A duk lokacin da gwamnati da kanta ta dabaibaiye tafiyar ƙasa, a ganina ya zama wajibi sojoji su ɗauki mataki domin riga kafi ga ɓarkewar fitina."


Da dama daga al´ummar ƙasar Mauritaniya na nunar da cewar tushen juyin mulki da ya kifar da Sidi Ould Cheik Abdullahi, shine irin yadda ya nisanta kansa daga mutanen da suka yi sanadiyar hawan sa kan karagar mulki, mussaman ma sojojin ƙasar.

Matakin da ya ɗauka na sauke shugabanin rundunonin sojojin ƙasar baki ɗaya kuma  a rana ɗaya,ba ƙaramin kuskure bane ya tafka, to saidai duk da haka  a cewar Diop Hamadu El Haji, wani mai kulla da harakokin siyasa a Mauritaniya, juyin mulki ba itace hanyar da ta cencenta ba,wajen warware matsalolin demokradiya.


"A tunanina, juyin mulki abun ne wanda ya kau a duniya, juyin mulki bai taɓa kawo ƙarshen wata matsala ba,illa ya daɗa dagula al´ammura.

Muddun mutane na kishin demokraɗiya, akwai hanyoyi iri- iri wanda tsarin mulkin demokraɗiya ya tanada, ta fannin warware rikici.

Wannan mataki da sojoji suka ɗauka zai jawo illoli masu yawa ta fannin siyasa da kuma tattalin arziki".


Haɗin gwiwar jam´iyu masu riƙe da ragamar  a ƙasar Mauritaniya, sun shirya taron gangami ,domin yin tur da Allah wadai ,ga wannan juyin mulki,  a yayin da yake bayyani akai, matamakin shugabanin wannan jam´yiu ,Alkahalil Ould Tayib yace.


"Mun yi imanin cewar Mauritaniya na cinkin matsayin zakaran gwajin dafi ta fannin tsarin mukin demokraɗiya.

Saboda haka, a halin da ake ciki yanzu,juyin mulki ga zaɓɓaɓen shugaba ya zama tsofan yayi.

Mun yi Allah wadai ga ɗaukar mulki ba ta hanyar demokradiya ba, kuma ba za mu taɓa amincewa ba, da wani shugaba, pace wanda aka zaɓa ta hanyar demokradiya".

....................................

A halin da ake ciki dai ra´ayoyi  sun bambamta a ƙasar Mauritaniya, tsakanin masu goyan baya da kuma masu adawa da juyin mulkin.

Saidai ƙasashen ƙetare da Ƙungiyoyin ƙasa baki ɗaya, sun yi Alah wadai da shi.

Ƙasar France wadda ta yi wa Mauritaniya mulkin mallaka, tayi kira ga sojojin su maida mulki ga hamɓaren shugaban cikin gaggawa.

Haka zalika,Kazalika, Ƙungiyar Tarayya Afrika, wadda har ma ta yanke hukunci fidda Mauritaniya daga matsayin memba.

A lokacin da yayi huruci akan batun, shugaban Tarayya Nigeria Al Haji Umaru Musa ´yar Adua, ya bayyana matsayin Nigeria da cewar:


" Nigeria ba za ta amincewa da duk wata gwamnati ba, pace wadda jam´a ta zaɓa ta hanyar kundin tsarin mulki.

Saboda haka,Nigeria ta yi tur da Allah wadai, ga juyin mulkin ƙasar Mauritaniya".


Wakilin Majalisar Ɗinkin Dinkin Duniya game da Nahiyar Afrika Said Jinnit, ya gana da komitin sojojin da ya shugabanci juyin mulki, ya kuma yi amfani da wannan dama, inda ya bayana matsayin Sakatare Janar na MajalisarƊinkin Duniya Ban Ki Moon na adawa da matakin hamɓara da zaɓɓaɓen shugaban ƙasa.


"Wannan koma baya ne ta fannin demokradiya.

Matsayin Majalisar Ɗinkin Duniya ba zai wuce ba na Ƙungiyar Tarayya Afrika, wato tofin Allah tsine ga juyin mulki.

Majalisar Ɗinkin Duniya tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Tarayya Afrika, za su duƙufa, domin lalubo hanyoyin maida Mauritaniya bisa tafarkin demokradiya."

A yayin ƙasashen duniya ke cigaba da yin Allah wadai ga wannan juyin shikuwa saban shugaban, Jannar Mohamed Ould Abdullahi kira yayi ga jama´ar ƙasa ta bashi haɗin kai:


"Ina kira ga ɗaukacin ´yan Mauritaniya su manta da ɗan sabanin ra´ayin ma wucewa, su duƙufa zuwa aiki, su kuma bada haɗin kai ga sabin shugabani a yunƙurinsun na warware matsalolin da ƙasa ke fama da su, wanda suka haɗa da yinwa, jahilci da cuttutuka.

A namu ɓangare, mun ɗauki alƙawarin gaggauta maido da tsarin mulkin demokradiya, da kuma yaƙi ba ji ba gani, da cin hanci da karɓar rashawa."


Juyin mulkin na ƙasar Mauritaniya babban ƙalubale ne ga Ƙungiyar Tarayya Afrika, a game da burinta, na inganta tsarin mulkin demokraɗiya a faɗin Nahiyar baki ɗaya.

Ayoyin tambaya a nan sune, shin AU za tayi amfani da ƙarfin soja kamar yadda ta yi a tsibirin Komoro ,domin cilastawa sojojin Mauritaniya sun lashe amensu,kokuwa Ƙungiyar Tarayya Afrika za ta bi hanyoyi na tattanawa ? Kwanaki masu zuwa zasu bada ƙarin haske.