Juyin juya halin siyasa a Pakistan | Labarai | DW | 28.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Juyin juya halin siyasa a Pakistan

Shirye shirye a Pakistan sun yi nisa dangane da rantsar da Mr Musharraf, a matsayin shugaban farar hula na ƙasar. A gobe Alhamis ne ake sa ran Mr Musharraf zai karɓi rantsuwar, a matsayin shugaban farar hula na Pakistan. Da safiyar yau ne Mr Musharraf ya ajiye kakinsa na soji, tare da mika muƙamin shugaban rundunar sojin ƙasar ga Janar Ashfaq Kiyani. Dokar ta ɓacin da Mr Musharraf ya kafa a ƙasar har yanzu na nan na aiki. A cewar Mr Musharraf, matakin zai taimaka wajen daƙile fitinar tsageru da ´Yan ta´adda dake cin karensu babu babbaka a ƙasar.