Juyayin ta′asar Auschwitz a MDD | Siyasa | DW | 25.01.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Juyayin ta'asar Auschwitz a MDD

A jiya litinin, a karo na farko MDD ta yi zaman tunawa da mutane sama da miliyan daya da aka kashe a sansanin gwale-gwalen Auschwitz a zamanin yakin duniya na biyu

Joschka Fischer a MDD

Joschka Fischer a MDD

A lokacin da yake jawabi ga mahalarta zauren babbar mashawartar MDDr, ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer wannan danyyen aiki na rashin imani da ‚yan Nzinhitler suka aikata zai ci gaba da zama tabo ga tarihin Jamus. Wannan ta’asar ce ta sanya kasar ta shigar da manufar girmama mutuncin dan-Adam a cikin shikashikan daftarin tsarin mulkinta a shekarar 1949. Ministan harkokin wajen na Jamus ya kara da cewar:

Sabuwar kasar Jamus da aka kafa a bisa sahifin tsarin mulki na demokradiyya ta koyi darasi daga wannan danyyen aiki ta kuma lashi takobin cewar har abada hakan ba zai sake faruwa a harabarta ba.

Fischer da sakatare-janar na MDD Kofi Annan sun tunasar cewar ita kanta majalisar dinkin duniyar an kirkiro ta ne domin a yi kandagarkin ire-iren wannan kisan kare-dangi shigen wanda aka yi wa Yahudawa. Sakatare-janar Kofi Annan ya kara da cewar:

Bai kamata irin wannan danyyen aikin ya sake faruwa ba. Wani abin da ya kamata a guje shi kuma shi ne kin amincewa da gaskiyar abin da ya faru ko kin mayar da martanin da ya dace.

Annan ya kara da cewar wannan maganar ta shafi har da lardin Darfur na kasar Sudan. Domin kuwa ire-iren abubuwan da aka fuskanta a Ruwanda da Kamboja da Kosovo suna masu bayyanarwa ne a fili cewar har yau duniya bata tsira daga wannan shaidanci ba. An ji irin wannan kashedin daga sauran jami’ai 35 da suka gabatar da jawabai lokacin zaman juyayin a zauren babbar mashawartar majalisar dinkin duniya a jiya litinin. Wannan zaman kuwa shi ne na farko da majalisar ta gudanar tun bayan kwaco fursinonin da aka yi daga sansanin gwale-gwale na Auschwitz shekaru 60 da suka wuce. A nasa bangaren Eli Wiesel, mai lambar yabo ta nobel dangane da marubuta adabi, wanda kuma ya shaidar da ta’asar kisan kiyashin ta ‚yan nazi ya kalubalanci sauran daulolin duniya irinsu Amurka, wadanda a ganinsa suka kasa tabuka kome domin hana wanzuwar wannan ta’asa. Ya ce a sakamakon ko oho da duniya tayi ne ‚yan Nazin suka samu damar cin karensu ba babbaka suna masu azabtar da fursinoni da yi musu kisan ba gaira. Ta la’akari da tabargazar da aka fuskanta a majalisar jihar Sachsen makon da ya gabata daga jam’iyyar NPD mai ra’ayi irin shigen na ‚yan Nazi, ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya ce kasar ba zata dadara ba tana mai bakin kokarinta wajen yaki da dukkan launi na wariyar jinsi da adawa da Yahudawa da kyamar baki a harabarta.