1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Juyayin sama da mutune 1000 a Bangaladash

Yusuf Bala Nayaya
April 24, 2018

Daruruwan mutane ne a kasar Bangaladash a wannan Talata sun yi biki da addu'oi na tunawa da sama da mutane 1,100 da suka rasu sakamakon ruftawar masana'antar dinke-dinke da ke a wajen birnin Dhaka shekaru biyar kenan.

https://p.dw.com/p/2waaz
Bangladesch 4. Jahrestag Einsturz Textilfabrik
Hoto: Getty Images/AFP

Kungiyoyi na 'yan kwadago da 'yan uwa da abokan wadanda suka rasa rayukansu a ruftawar masana'antar sun nemi da a samar da tallafi na kudi ga iyalan mamatan da suka bakunci lahira bayan rufatawar ginin Rana Plaza mai hawa takwas, lamari da ya faru a ranar 24 ga watan Afrilu na shekarar 2013.

Har ila yau sun kuma nemi da a samar da kulawar lafiya ga wadanda lamarin ya shafa ganin yadda da dama daga cikinsu ke ci gaba da fiskantar nau'ika na kalubale sakamako na raunika ko nakasa da suka samu a hadarin ruftawar ginin masana'antar. 'Yan sanda a Bangaladash sun tuhumi mai ginin masana'antar ta Rana da wasu kamfanoni da lafin haddasa kisan kai, sai dai har yanzu ba a kai ga rufe mai masana'antar ba.