1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jos: Gwamnatin za ta mayar da 'yan gudun hijira gida

Abdullahi Maidawa Kurgwi
June 1, 2018

Gwamnatin Filato ta soma aiki da umurnin shugaban kasa game da shirin maido da dubban jama’a da suka rasa muhallansu sakamakon tashe-tashen hankula mussaman ma rigingimu na makiyaya da manoma.

https://p.dw.com/p/2yosC
Nigeria UN Camp in Maiduguri
Hoto: imago/epd/A. Staeritz

Yanzu haka ma dai akwai wani kwamitin tuntuba da zai rika ganawa da al'ummomi da tashe-tashen hankula ya raba su da muhallansu a wasu jihohi shida ciki harda jihar Filato kamar yadda gwamnan Filato Simon Lalong ya sheda min.

To sai dai kuma al'ummar Berom na jihar Filato na cigaba da korafin cewar har yanzu ana kai musu hare hare mussaman ma a kauyuka na yankin Barkin Ladi da ma wasu yankuna da suke zama.

Nigeria Flüchtlinge
Wadanda suka rasa matsugunnensuHoto: Malik Samuel/Ärzte ohne Grenzen

Cikin wata ganawa da manema labarai a Jos, shugabar kungiyar mata yan kabilar Berom Ngo Florence Dachollom Jambo ta ce yanzu haka akwai kimanin 'yan kabilar Berom dubu 33 da wannan rikici ya raba su da muhallansu kuma har yanzu abin bai tsaya ba a cewar ta.

A bangare guda kuma shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Filato Nura Abdullahi ya ce suma al'ummar Filani su na fama da matsalar sace-sacen shanu inda domin ko a makon nan sun yi fama da wannan matsala a karamar hukumar Barkin Ladi. To sai kuma ya ce suna goyon bayan duk wani mataki na zaman lafiya da gwamnati zata dauka yanzu.