Jordan ta yi alkawarin ci gaba da tallafa wa al’umman Falasɗinu. | Labarai | DW | 25.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jordan ta yi alkawarin ci gaba da tallafa wa al’umman Falasɗinu.

Sarki Abdallah na ƙasar Jordan, ya yi alkawarin ci gaba da tallafa wa Falasɗinawa har zuwa lokacin da suka sami ’yanci suka ƙaddamad ƙasarsu mai cin gashin kanta. Sarkin ya yi wannan jawabin ne a bikin cika shekaru 60 da samun ’yancin ƙasarsa daga Ingila.

Manazarta al’amuran yau da kullum a yankin Gabas Ta Tsakiya sun ce Sarkin ya yi jawabin ne wata ɗaya, bayan da jami’an tsaron Jordan ɗin suka gano wata maɓuyar makamai a ƙasar, a cikinsu har da rokokin nan na Katyusha, ƙirar Iran, waɗanda aka jiɓinta su da wasu ’yan Ƙungiyar Hamas guda 20 da aka tsare. Jordan na zarginsu ne da shirin kai wa jami’anta da kafofinta hare-hare, abin da ƙungiyar ta Hamas ta musanta.