Jordan ta ba da sunayen ´yan Iraki 4 da suka kai mata harin ta´addanci | Labarai | DW | 13.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jordan ta ba da sunayen ´yan Iraki 4 da suka kai mata harin ta´addanci

Gwamnatin Jordan ta ba da sunayen ´yan Iraqi 4 maza 3 da mace daya da ke da hannu a hare haren kunar bakin wake da aka kai kan wasu manyan otel-otel a birnin Amman. Mukaddashin FM Marwan al-Muasher ya ce matar wadda ta kasa ta da bam din a jikinta kuma yanzu haka ta ke hannun hukuma, ita ce matar daya daga cikin maharan kuma ´yar´uwar wani laftanan ne na Abu Musab al-Zarqawi shugaban kungiyar al-Qaida a Iraqi. Dukkan maharan 3 sun mutu a harin wanda yayi sanadiyar rayukar mutane 57. Muasher ya fadawa wani taron manema labarai cewa ´yan ta´addan sun shiga cikin kasar ta Jordan kwanaki 4 gabanin kai harin a ranar laraba da ta gabata. Muasher ya ce matar ta raka mijinta zuwa wani zauren bikin aure a daya daga cikin otel-otel din amma da bam din ta ya ki fashewa sai mijinta ya tura ta waje kafin ya ta da nashi. Kungiyar al-Qaida a Iraqi karkashin jagorancin dan Jordan Abu Musab al-Zarqawi ta yi ikirarin kai hare haren.