Jonathan ya rusa majalisar ministocin Nijeriya | Labarai | DW | 17.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jonathan ya rusa majalisar ministocin Nijeriya

Muƙaddashin shugaban Nijeriya ya rusa majalisar ministocin ƙasar, bayan taronta na mako-mako

default

Muƙaddashin shugaban Nijeriya, Dakta Goodluck Jonathan.

Muƙaddashin shugaban Nijeriya, Dakta Goodluck Jonathan, ya rusa majalisar ministocin ƙasar da yammacin larabar nan, kimanin wata guda kenan bayan da ya karɓi ragamar tafiyar da harkokin mulkin Nijeriya, biyo bayan tsawon lokacin da shugaban ƙasar, Alhaji Umaru Musa 'Yar'adua ya ɗauka yana jinya. Ministar kula da harkokin yaɗa labarai - mai barin gado a Nijeriya, Farfesa Dora Akunyili, wadda ta yiwa manema labarai jawabi bayan taron mako-mako na majalisar zartarwar ƙasar, ta ambata cewar, " A yau, muƙaddashin shugaban tarayyar Nijeriya Goodluck Ebele Jonathan, ya rusa majalisar ministocin tarayyar ƙasar. "

Ministar ta ƙara da cewar, ba za'a sami wani giɓi ba a harkar mulki, domin kuwa manyan sakatarori a ma'aikatun gwamnati ne zasu kula da sha'anin mulki, inda ta ce, ita ma zata miƙa ragamar tafiyar da ma'aikatar yaɗa labarai ne ga babban sakatare a ma'aikatar.

Matakin rusa majalisar ministocin dai, ya zo ne a dai-dai lokacin da wani sabon rikicin daya ɓarke a ƙauyen Riyom dake kusa da Jos, babban birnin jihar Filato ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Sai dai kuma tuni hukumomin tsaro a ƙasar suka bayar da tabbacin bada kariya ga rayuka da dukiyar jama'a bayan rikicin baya-bayannan.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Ahmad Tijani Lawal